Halin da Wasu Ƴan Najeriya Ke ciki a Gidan Gyaran Hali na Saudiyya
- Jakadan Najeriya a Saudiya, Dakta Yakubu Gambo, ya bayyana dalilin da ya sa wasu ’yan Najeriya na ci gaba da zama a gidajen yari
- Gambo ya ce wasu ’yan Najeriya da suka kammala hukuncin daurin su na fuskantar matsalar komawa gida, yayin da jakadanci ke ba da takardun tafiya na gaggawa
- Abike Dabiri-Erewa ta tabbatar da ci gaba da haɗin gwiwa da jakadancin Najeriya, tare da kira ga ’yan Najeriya a Saudiya su yi rajista domin inganta hulɗa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudiyya - Jakadan Najeriya a Masarautar Saudiya, Dakta Yakubu N. Gambo, ya nuna damuwa kan halin da wasu ’yan Najeriya ke ciki a Saudiyya.
Gambo yana magana ne kan halin da yan kasarsa ke ciki a gidajen yari da cibiyoyin tsare mutane a ƙasar.

Source: Twitter
Gambo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin ziyarar da ya kai wa Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Hon. Abike Dabiri-Erewa, a hedikwatar hukumar da ke Abuja, cewar Vanguard.
Najeriya ta magantu kan ƴan ƙasar a Saudiyya
A cikin wata sanarwa da Violet Nwosu, jami’ar hulɗa da jama’a da kafofin yaɗa labarai ta NiDCOM, ta sanya wa hannu, jakadan ya ce batutuwan da suka shafi ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci tun bayan da ya fara aiki.
Ya ce manufofin harkokin wajen Najeriya sun ba da muhimmiyar kulawa ga jin daɗin ’yan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje.
Gambo ya ce ofishin jakadancin ya umarci ƙungiyoyin ’yan Najeriya daban-daban da ke Saudiya su haɗa kai ƙarƙashin ƙungiya guda, domin inganta haɗin kai da sauƙaƙa hulɗa da jakadancin.
Ya ce:
“Ofishin ya umarci ƙungiyoyin ’yan Najeriya daban-daban su tsara kansu ƙarƙashin ƙungiya guda domin samar da haɗin kai da bai wa jakadanci damar magance batutuwan da suka shafi ’yan Najeriya yadda ya kamata.”

Source: Twitter
Kokarin gwamnati kan ƴan Najeriya
A halin da ake ciki, Gambo ya ce sabanin yadda ake yawan zato, Saudiya na da ’yan Najeriya da dama da suka yi fice a sana’o’insu, ciki har da likitoci, injiniyoyi, malamai, ’yan sana’a da ’yan kasuwa.
Ya ce akwai kuma iyalan ’yan Najeriya da suka shafe shekaru da dama suna rayuwa a Masarautar, cewar Punch.
Jakadan ya kuma yi magana kan halin da wasu ’yan Najeriya ke ciki a gidajen yari da cibiyoyin tsare mutane.
“Muna kuma fuskantar ƙalubalen da suka shafi ’yan Najeriya da ke gidajen yari da cibiyoyin tsare mutane, ciki har da waɗanda suka kammala hukuncin daurin su amma ba sa iya komawa gida saboda tarar da ake binsu.”
- Gambo
Jakadan ya ce Ofishin Jakadancin Najeriya ya sake umartar ƙungiyoyin ’yan Najeriya daban-daban da ke Saudiya su haɗa kai ƙarƙashin ƙungiya guda domin inganta haɗin kai da sauƙaƙa warware matsalolin da ke damun ’yan Najeriya.
An kashe yan Najeriya a Afirka ta Kudu
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da kisan wasu 'yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu, tare da neman a gudanar da bincike.
Kasar ta nuna damuwa kan karuwar hare-haren ƙyamar baƙi, tana gargadin cewa ci gaba da hakan na iya lalata dangantakar Najeriya da Afirka ta Kudu.
Najeriya ta bukaci 'yan kasarta su kwantar da hankali, su guji ɗaukar doka a hannu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya.
Asali: Legit.ng


