Emmanuella da sauran kananan yara 5 mafi shahara da suka fi sa'annin su kudi a Najeriya

Emmanuella da sauran kananan yara 5 mafi shahara da suka fi sa'annin su kudi a Najeriya

Da wuya a samu wanda ya tashi ba tare da sha'awara tara da dukiya ba kuma dai Hausawa na cewa arziki kashi ne, a yayin da an samu wasu mashahuran kananan yara a Najeriya da suka tako shi tun kafin su kai shekarun samartaka.

Babu shakka akwai wasu jerin kananan yara shida da suka shahara a kan sana'ar nishadantarwa kama daga wake-wake da kuma barkwanci, lamarin da ya sanya suka samu nasibi wajen tara dukiya mai yawan gaske tun kafin su gama sanin ciwon kawunansu.

A wani rahoto da muka kalato daga jaridar The Nation, jerin wadannan yara shida na ci gaba da baje nasibi musamman a fagen nishadantarwa da a yanzu sun shahara a Najeriya cikin kankanin lokaci.

Ga sunayensu, yawan dukiya da suka mallaka da kuma sana'ar da suka dabi'antu da ita:

1. Emmanuella Samuel

An haifi Emmanuella a ranar 22 ga watan Yulin 2010. Ta fara sana'ar barkwanci tun tana 'yar shekara biyar. A yanzu ta shahara wajen watsa faifan bidiyoyi daban-daban na barkwanci a shafin YouTube.

Emmanuella tana da tarin dukiya wadda ta kai kimanin dalar Amurka 90,000 wato fiye da Naira miliyan 20 a ma'aunin kudi na Najeriya.

2. Ahmed Star Boy

Ahmed wanda bai wuce shekaru 13 ba a duniya yana da tarin dukiya ta kimanin naira miliyan 10 wadda ya samu a sanadiyar haduwarsa ta fitaccen mawakin nan na Najeriya, Wizkid.

3. Destiny Boy

Afeez Adesina wanda aka fi sani da Destiny Boy, yana da kimanin naira miliyan 8 a sanadiyar haduwarsa da mawakin nan na Najeriya da ya shahara musamman a wurin matasa wato Davido.

4. DJ Young Money

Young DJ na daya daga kananan yara mafi shahara a Najeriya wanda shekarun sa na haihuwa ba su wuce 12 ba. Ya shahara wajen kade-kaden wakoki inda ya ke da tarin arziki na kimanin naira miliyan 20.

5. Egypt Ify Ufele

Ify wadda aka haifa a ranar 3 ga watan Mayun 2005, ta kware a kan sana'ar dinkin kayayyaki musamman na 'yar tsana wato 'bebin roba' wadda ta samu nasibi mai girman gaske a sanadiyar sha'awa da kuma tsayuwar daka kan sana'ar dinki da ta ke matukar marari.

A sanadiyar kiba da nauyin jiki, matsananciyar cutar Asma ta kama Ify wadda a kullum take kan hanyar zuwa asibiti, lamarin da ya sanya kawaye da abokai suka rinka tsangwama da tsokanarta a makaranta.

Duk da wannan kalubale na rayuwa da Ify ta fuskanta, a halin yanzu tana da tarin dukiya wadda ta kai kimanin naira miliyan 10.

KARANTA KUMA: Kungiyar kwadago reshen jihar Kebbi ta ki amincewa da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

6. OzzyBosco Wonderkid

Bosco wand aka haifa a ranar 7 ga watan Janairun 2007, ya yi shaharar gaske a kan sana'ar waka wanda a halin yanzu yana da tarin dukiya ta kimanin naira miliyan 20. Shaharar da Bosco yayi ya sanya ana alakanta shi da wasu fitattun mawaka kamar D’Banj da Naeto C.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel