Sunan Minista Ya Fito a Jerin Wadanda Aka Tsara Neman Tallafinsu don Yiwa Tinubu Juyin Mulki

Sunan Minista Ya Fito a Jerin Wadanda Aka Tsara Neman Tallafinsu don Yiwa Tinubu Juyin Mulki

  • Wani tsohon kyaftin din ruwa da ake tuhuma kan zargin shirin juyin mulki ya ce ya san da shirin amma bai goyi bayansa ba
  • Erasmus Victor ya ce ya sha gargadin Kanal Mohammed Ma’aji kan dakatar da shirin amma bai saurare shi ba
  • Wanda ake zargin ya bayyana sunan ministan Tinubu sa aka tsara za a nemi talafin kudi daga wurinsa don kifar da shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani tsohon kyaftin din ruwa da ake tuhuma kan zargi da hannu a shirin juyin mulki ya bayyana abubuwan da ya sani.

Idan baku manta ba an kama wasu sojoji da wadanda suka yi ritaya bisa zargin shirya hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bara.

Kanal Ma'aji.
Kanal Muhammad Ma'aji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Bayanan da Premium Times ta samu ta bayan fage sun kunshi bayanin Erasmus Victor, wanda yana daga cikin mutum shida da ake tuhuma a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin shirin juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun gana da Tinubu sun masa zafafan kalamai kan Najeriya

An kara samun bayanai kan shirin juyin mulki

A cikin bayaninsa, Victor, wanda ya koma siyasa bayan barin aikin soja, ya amince cewa ya tattauna batun shirin juyin mulki da Kanal Mohammed Ma’aji sau da dama ta hanyar manhajar aika sakonni.

Ya kuma ce sun taba yin barkwanci kan yiwuwar samun mukamai a gwamnati idan shirin ya yi nasara.

Sai dai ya jaddada cewa duk da cewa bai kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro ba, bai taba goyon bayan shirin ba.

Ya ce abin da ya yi shi ne ya nuna kamar yana taimaka wa Ma’aji ne domin samun damar shawo kansa ya yi watsi da batun.

Yadda aka rika neman masu daukar nauyi

Victor ya shaida cewa ya ci gaba da rokon Ma’aji ya yi watsi da batun juyin mulki amma daga baya kanal din ya sanar da shi cewa yana bukatar masu hannu da shuni da za su dauki nauyin gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

Victor ya ce Ma’aji, mai shekaru 50 daga Bida a Jihar Neja, ya ambaci wasu manyan mutane tare da neman ya tuntube su a madadinsa.

Daga cikin mutanen da aka ambata akwai Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, Nyesom Wike.

An ambaci sunan ministan Abuja

Victor ya ce ya sanar da Ma’aji cewa Wike shi kadai ne daga cikin sunayen da ya sani da kansa, kuma ya ba shi shawarar idan yana son tuntubarsa ya yi hakan kai tsaye.

Ya ce:

“Na rike shugaban karamar hukumar Ogu/Bolo karkashin Nyesom Wike, kuma na bar mulki a 2021. Ya ba da shawarar in shigar da Nyesom Wike cikin shirin domin neman kudi daga gare shi.”

Ya kara da cewa bai taba tuntubar wani daga cikin mutanen da aka ambata ba, ciki har da Wike.

A maimakon haka, ya ce kawai ya sanar da Ma’aji cewa bai samu nasarar nemo masu daukar nauyin juyin mulkin ba.

Yadda aka raba kudin tsara juyin mulki

An ji cewa masu bincike sun zargi tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da bayar da gudunmuwar kuɗi domin yunkurin juyin mulkin 2025 ta hannun wani kamfani

Rahotanni sun ce an raba sama da N700m ga jami'an soja, malamai da wasu fararen hula bisa umarnin Kanal Mohammed Ma'aji

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262