Najeriya Ta Yi Gargadi kan Yakin Houthi da Saudi, Ta Fadi Me Take So a Yi
- Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da sabon harin da mayakan Houthi suka kai kan wuraren fararen hula a yankin Najran na Saudiyya
- Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce harin da ya jikkata fararen hula, ciki har da mata da yara, abin da ya take dokokin ƙasa da ƙasa ne
- Najeriya ta yi kira ga dukkan ɓangarorin rikicin da su yi taka-tsantsan tare da ƙarfafa ƙoƙarin diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da sabon harin da mayakan Houthi na Yemen suka kai kan wuraren fararen hula a yankin Najran na ƙasar Saudiyya.
Gwamnatin ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin da su bi a hankali tare da sake mayar da hankali kan tattaunawar diflomasiyya domin kawo ƙarshen tashin hankalin.

Source: Facebook
A sakon da ta wallafa a Facebook, Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana harin a matsayin babban take dokokin ƙasa da ƙasa, musamman waɗanda suka tanadi kariyar fararen hula a lokacin yaƙi.
Maganar kai hari Saudi
A cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce harin da aka kai a Najran ya jikkata fararen hula da dama, ciki har da mata da yara.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi matuƙar damuwa da yadda rikicin ke ƙara tsananta, tana mai jaddada matsayinta na adawa da duk wani hari da ake kai wa fararen hula ko muhimman abubuwan more rayuwa.
Ta ce kai wa fararen hula da gine-ginen da suke amfani da su hari da gangan abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma ya kamata al'ummar duniya ta yi Allah wadai da irin waɗannan hare-hare ba tare da la'akari da wanda ya aikata su ba.
Kira ga ƙoƙarin diflomasiyya
Radio Nigeria ta wallafa cewa Najeriya ta buƙaci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su yi matuƙar taka-tsantsan, su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa tare da ba da fifiko ga kare rayukan fararen hula.
Gwamnatin ta kuma yi kira da a ƙara ƙoƙarin diflomasiyya domin cimma matsaya mai ɗorewa da za ta kawo zaman lafiya, tare da mutunta ikon mallaka, cikakken yankin ƙasa da tsaron dukkan ƙasashen yankin.

Source: Getty Images
Ma'aikatar ta ce Najeriya na sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa, kuma za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulɗarta na yankin da na ƙasa da ƙasa domin inganta zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya.
Batun yakin Iran da Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa babban hafsan sojin Amurka, Janar Dan Caine, ya tattauna da wasu manyan jami'an gwamnatin Donald Trump kan buƙatar nemo hanyar da Amurka za ta fita daga yaƙin da take yi da Iran.
Majiyoyi sun ce Caine na ganin cewa wasu matakan soji da ake nazari domin ƙara tsananta rikicin na iya jefa Amurka cikin ƙarin matsala, yayin da hare-haren sama kaɗai ba za su iya cimma manufofin Trump ba.
An ce babban hafsan ya tattauna wannan batu da Daraktan CIA John Ratcliffe, Ministan Harkokin Waje, Marco Rubio da Mataimakin Shugaban Ƙasa JD Vance, yayin da yake ƙoƙarin ganin an fahimci iyakokin matakan soji da ake da su.
Asali: Legit.ng

