Kungiyar kwadago reshen jihar Kebbi ta ki amincewa da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Kungiyar kwadago reshen jihar Kebbi ta ki amincewa da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Murna ta koma ciki a yayin da kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kebbi, ta ki amincewa da hukuncin da gwamnatin jihar ta dauka ita kadai a kashin kanta kan mafi karancin albashin ma'aikata.

Rassan kungiyar kwadagon guda uku bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Talata, ta ce ba ta da hannu a sanarwar da sakataren gwamnatin jihar ya gabatar dangane da fara biyan ma'aikatan jihar mafi karancin albashi na N30,000.

Kungiyar ta ce hukuncin da gwamnatin jihar ta zartar ya sabawa ka'idodin yarjejeniyar da ta kulla a tsakaninta da ita, lamarin da ta ce ba ta da alaka da shi.

A rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, kungiyar ta bukaci sabon mafi karancin albashi ya hadar har da ma'aikata da ke gaba da mataki na bakwai sabanin yadda ta kaddamar a yanzu inda zai shafi ma'aikata dake matsayi na daya zuwa na shida.

Kungiyar ta kirayi gwamnatin jihar Kebbi da ta kaddamar da wani kwamiti domin aiwatar da aiki na lura kan fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata da dukkanin bangarori zasu amince da shi.

KARANTA KUMA: Samson Siasia ya nemi a kawo masa dauki kan mahaifiyarsa da masu garkuwa suka sace

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Litinin da ta gabata ne sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Babale Yauri, yayin ganawa da manema labarai cikin Birnin Kebbi ya sanar da cewa, gwamnatin jihar za ta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata na N30,000 a watan Satumba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng