Tun ina 'yar shekara 12 mijin mahaifiyarmu yake kwanciya dani da kanwata - Wata budurwa ta sanar da kotu

Tun ina 'yar shekara 12 mijin mahaifiyarmu yake kwanciya dani da kanwata - Wata budurwa ta sanar da kotu

- Wata budurwa ta kai kukanta wajen Alkali akan irin abinda mijin mahaifiyarsu yake yi musu ita da kanwarta

- Ta bayyana cewa mijin mahaifiyar ta su yana kwanciya da su duka su biyu ita da kanwarta

- Ta kara da cewa tun tana 'yar shekara 12 yake kwanciya da ita idan taje kaiwa mahaifiyarta ziyara gidan shi

Wata mata dake zaune a garin Ibadan mai suna Esther Isaiah, ranar Larabar nan ta zargi mijin mahaifiyarsu mai suna John Dickson, da yi mata fyade ita da kanwarta.

Da take sanar da hakan a wata kotu dake Mapo a garin na Ibadan, Isaiah mai shekaru 20 ta kuma zargi cewa mijin mahaifiyarsun shine yasa tarbiyarta ta lalace.

"Mijin mahaifiyar mu ya fara kwanciya dani tun ina 'yar shekara 12 ni da kanwata, duk lokacin da muka kaiwa mahaifiyarmu ziyara gidan da take auren shi.

"Duk lokacin da mahaifiyarmu ba ta gida, yana yi mini barazanar cewa zai kashe ni idan har ban barshi ya kwanta dani ba, ni kuma hakan yake sawa na kwanta dashi saboda ina tsoron mutuwa.

"Yayi min fyade a lokuta da, ban taba sanar da mahaifiyata ba saboda ina tsoron ko wani abu zai faru, amma na sha sanar da abokaina.

"Ya kuma yiwa kanwata fyade, ta taba sanar dani cewa ya taba shigowa dakin da take yin bacci fuskar shi a rufe yayi mata fyade ya fita," in ji ta.

KU KARANTA: Allah Sarki: An kama wani karamin yaro Musulmi dan shekara 4 saboda ya jefi motar 'yan sanda a kasar Isra'ila

Sai dai shi kuma Dickson ya bayyana cewa yayi hakan ne saboda matar shi bata bari ya kwanta da ita, ya ce matar tashi taki yarda ta kwanta dashi na tsawon shekara uku.

Ita kuma mahaifiyar yaran mai suna Mary ta bayyana cewa, kwarai bata kwanciya dashi saboda azzalumin mutum ne kuma dabba ne shi kawai anyi shi ne a cikin mutane.

"Kwarai da gaskee na bar mishi gidanshi, ya yiwa 'yata fyade, daya daga cikin 'ya'yan dana haifa kafin na aure shi.

"Yarinyar tana tsoron sanar dani abinda mijin nawa yayi mata, kuma ta daina ziyarta ta.

"a garin dana fito jihar Cross River, babbar matsala ce mutum ya kwanta da 'yar gidan matar shi da kuma mahaifiyarta."

Bayan alkalin kotun ya kammala sauraron korafin nasu, alkalin kotun Cif Ademola Odunade, ya bukaci mutanen da su yi abubuwan da suka kamata.

Ya kuma bayyana za su kama Dickson da laifin fyade. Sannan kuma ya daga sauraron karar zuwa 15 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel