Fitattun Yan TikTok 3 Sun Fara Ganin Sakamako bayan Sun Taba Mutuncin Shugaban Kasa

Fitattun Yan TikTok 3 Sun Fara Ganin Sakamako bayan Sun Taba Mutuncin Shugaban Kasa

  • An yanke wa wasu fitattun yan TikTok uku hukuncin daurin watanni biyu zuwa uku a gidan yari a kasar Senegal
  • Haka zalika kotu ta ci tarar CFA 500,000 kan fitattun yan TikTok din bayan ta same su da laifin cin mutuncin Shugaba Bassirou Diomaye Faye
  • Lauyan wadanda ake zargin ya ce bidiyoyin ba su kai ga matakin gurfanar da su a gaban kotu ba, domin lamari ne na barkwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Senegal - Wata kotu a Senegal ta yanke wa wasu fitattun masu amfani da TikTok uku hukuncin dauri a gidan yari tare da cin tarar biyu daga cikinsu.

Kotun ta yanke musu wannan hukunci ne bayan an same su da laifin cin mutuncin shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, lamarin da ya jawo suka daga masu rajin kare ‘yancin fadin albarkacin baki.

Kara karanta wannan

An matsawa shugaban EFCC lamba ya sauka ko Tinubu ya kore shi

Bassirou Diomaye Faye.
Shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye a fadarsa Hoto: Bassirou Diomaye Faye
Source: Facebook

Siyasa ta dauki zafi a Senegal

A rahoton Reuters, mutane ukun na da alaka da Feenal Digital, wani dandali na sadarwa na yanar gizo da ke samar da abubuwan da wasu masu sa ido ke ganin suna nuna goyon baya ga tsohon Firaminista Ousmane Sonko da jam’iyyarsa ta PASTEF.

Shari’ar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun karin rikicin siyasa bayan Sonko ya rabu da Shugaba Faye, wanda a baya abokinsa ne kuma suka yi tafiya tare a siyasa.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Kasa Faye ya kaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa a watan da ya gabata.

Feenal Digital ta bayyana kanta a Facebook a matsayin dandali da ke inganta ayyukan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

Hukuncin da aka yanke wa yan TikTok 2

Kotun ta yanke wa Mandoumbe Diop, daya daga cikin yan TijTok din wanda aka fi sani da Lamignou Darou, hukuncin daurin watanni uku a gidan yari ba tare da dakatar da hukuncin ba.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya shiga tsaka mai wuya kan rufe asusun gwamnati da umarnin Tinubu

Diop shi ne wanda ya fi shahara cikin mutanen ukun, inda yake da mabiya sama da 500,000 a TikTok. Bidiyoyinsa kan samu dubban kallon jama’a akai-akai.

Sauran yan TikTok din, Magueye Diaw, wanda aka fi sani da Oustaz Thiep, da Moustapha Ndiaye, wanda aka fi sani da Ndiaye Touba, kowannensu an yanke masa hukuncin daurin watanni biyu.

Lauya ya kare abubuwan da suka wallafa

Lauyan mutanen, Abdy Nar Ndiaye, ya kare abubuwan da suka wallafa da suka jawo gurfanar da su a gaban kotu.

Ya bayyana bidiyoyin TikTok din a matsayin na “ban dariya”, yana mai cewa bai kamata su kai ga gurfanar da masu wallafa su a gaban kotun aikata laifuka ba.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a kotuna Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kara da cewa an kuma ci tarar Diaw da Ndiaye CFA 500,000, kwatankwacin dala 800, kowannensu.

Lamarin ya kuma janyo hankali kan yanayin ‘yancin fadin albarkacin baki a Senegal, daya daga cikin kasashen dimokuraɗiyya da ake sa ido sosai a Yammacin Afirka.

Kotu ta daure 'yan TikTok a Ghana

Kun ji cewa wata mai amfani da TikTok a Ghana, Camilla Alhassan, ta gamu da hukuncin ɗaurin shekara guda saboda yaɗa labaran ƙarya.

Majiyoyi sun ce ana zarginta da wallafa labaran ƙarya da kuma kalaman batanci game da Shugaba John Mahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262