Tinubu Ya Aika Sako cikin Kaɗuwa da Aka Tabbatar da Rasuwar Babban Malami a Najeriya

Tinubu Ya Aika Sako cikin Kaɗuwa da Aka Tabbatar da Rasuwar Babban Malami a Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar fitaccen limamin coci a Najeriya, Fasto Emmanuel Abiodun Alogbo
  • Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tawali’u da imani wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta zaman lafiya da hadin kai
  • Shugaban kasar ya bukaci iyalan marigayin da mabiya cocin Cherubim and Seraphim su yi hakuri da wannan rashi da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An tabbatar da mutuwar babban limamin coci a Najeriya, Fasto Dr Emmanuel Abiodun Alogbo, shugaban darikar Cherubim and Seraphim Movement Church Worldwide.

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi jimamin rasuwar malamim, yana bayyana ta a matsayin babban rashi ga kiristoci da wadanda suka amfana da gudunmawarsa.

Shugaba Bola.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba

Tinubu ya shiga cikin miliyoyin mabiya addinin Kirista a Najeriya da sauran sassan duniya wajen jimamin rasuwar fitaccen shugaban addinin.

Wane irin mutum ne Alogbo?

A cewar Tinubu, rayuwar Fasto Alogbo ta kasance cike da tawali’u, tsayuwar imani da kuma jajircewa wajen kula da rayuwar ibada ta mabiya addini da kuma ci gaban kasa.

Tinubu ya ce irin gudunmawar da Alogbo ya bayar ta taimaka wajen samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

“Ta hanyar shugabancinsa na kwarai, Annabi Alogbo ya yi kokarin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da sulhu a tsakanin al’ummar Cherubim and Seraphim, tare da samun mutuntawa daga Kiristoci da masu bin sauran addinai,” in ji Tinubu.

Shugaban kasar ya ce gudunmawar Alogbo wajen karfafa zumuncin Kiristoci da samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin addini da al’umma za ta ci gaba da zama abin koyi ga tsararraki masu zuwa.

Wane sako Bola Tinubu ya aika?

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya yi barazana ga Tinubu, zai yi murabus daga jam'iyya mai mulki

Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabanni da mabiya cocin Cherubim and Seraphim Movement, da kuma duk wadanda rasuwar FastonAlogbo ta shafa.

Ya bukaci wadanda ke jimamin rasuwar da su yi hakuri tare da samun kwarin gwiwa daga kyawawan dabi’u da manufofin da marigayin ya bar baya.

Shugaban kasar ya kuma yi addu’ar Allah Ya bai wa ruhin limamim cocin, wanda ya bayyana a matsayin bawan Allah mai aminci, hutu na har abada.

Prophet (Dr) Emmanuel Abiodun Alogbo
Babban limamim coci a Najeriya, Fasto Emmanuel Abiodun Alogbo Hoto: Patience Ifemi
Source: Facebook

Tarihin kungiyar Cherubim da Seraphim

Cherubim and Seraphim na daga cikin manyan kungiyoyin Kiristanci da suka dade suna taka rawa wajen yada koyarwar Kiristanci da kuma ayyukan ibada a Najeriya.

Kungiyar tana da mabiya a sassa daban-daban na Najeriya, inda shugabanninta ke taka rawa wajen jagorantar ayyukan ibada da kuma karfafa zaman lafiya da hadin kai tsakanin mabiya.

Malamin musulunci ya rasu a jihar Borno

A wani labarin, an ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Mallam Haruna Dazigau Tijjani, ya riga mu gidan gaskiya a jihar Borno.

Wani matashi, Ibn Maigana ya sanar da rasuwar malamin, yana bayyana shi a matsayin mashahurin malami da ya ilmantar tare da tasiri ga al'ummar Bolori.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262