An kama kurtun soja da kananan buhunhunan tabar wiwi 169 a Jigawa

An kama kurtun soja da kananan buhunhunan tabar wiwi 169 a Jigawa

Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa sun kama wani jami'in soja, mai mukamin Kofural, da wasu kananan buhunhuna 169 dauke da ganyen tabar wiwi a karamar hukumar Ringim. An kama sojan tare da wasu mutane hudu dake aiki tare da shi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bala Zama Sanchi, ne ya bayyana hakan yayin da yake bajakolin jami'in sojan, Kofural Muzambilu Abdullahi, a hedikwatar 'yan sandan jihar Jigawa da ke garin Dutse.

Sanchi ya ce jami'an rundunar 'puff adder' ne suka kama sojan yayin da suke sintiri, tare da bayyana cewa dubun sojan ta cika ne bayan motar da ya dauko tabar wiwin ta yi hatsari a garin Maigatari da ke daf da iyakar Najeriya da Nijar.

Kwamishinan ya kara da cewa sojan kadai jami'an 'yan sanda suka samu, sanye da kakinsa, a wurin da motar ta yi hatsari.

Bayan jami'an 'yan sanda sun binciki motar ne sai suka ga kananan buhunhunan tabar wiwi makare a cikinta, a cewar Sanchi.

DUBA WANNAN: Wata uwa a Najeriya ta fadi dalilin da yasa ta amince dan cikinta ya yi mata ciki

Kwamishinan ya cigaba da cewa daga baya sun fahimci cewa an dauko hayar sojan ne a matsayin dan rakiyar tabar wiwin da za a kai garin Maigatari.

Ya ce sojan ya musanta cewa bai san menene cikin motar ba, tare da bayyana cewa bincikensu ya gano cewa tabar mallakar wani mutum ce mai suna Alhaji Abubakar, wanda tuni ya gudu bayan samun labarin abinda ya faru.

Kazalika rundunar 'yan sandan ta ce ta kama wasu mutane biyu; Nurah Mohammed da Abubakar A. Ahmed, mazauna garin Gumel, a wurin da motar ta yi hatsarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel