An Bude Shafin da Kowane Dan Najeriya Zai Iya Samun Tallafin N50,000, An Jero Abubuwan da Ake Bukata
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar SMEDAN ta sake bude shirin ba da tallafin N50,000 ga kananan 'yan kasuwa a Najeriya
- Tallafin ba rance ba ne, kuma ba a bukatar a mayar da kudin amma sna bikatar masu cin gajiyar shirin dole ne su dauki akalla mutum daya aiki
- Gwamnatin ta karfafa masu neman tallafin su cike bayanansu daidai a lokacin neman tallafin kamar yadda aka bukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kananan 'yan kasuwa a Najeriya sun samu sabuwar dama ta samun tallafin gwamnati bayan Hukumar Bunƙasa Kananan da Matsakaitan Masana'antu ta Najeriya (SMEDAN) ta sake bude shirin tallafin CGS.
Shirin na bai wa masu gudanar da kananan sana'o'i da kasuwanci tallafin sau daya na N50,000, wanda ba rance ba ne kuma ba a bukatar a mayar da kudin.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a

Source: Facebook
Vanguard ta ruwaito cewa an tsara tallafin ne domin taimaka wa kananan 'yan kasuwa wajen inganta harkokinsu, fadada kasuwanci da kuma samar da karin guraben ayyukan yi.
Sharadin samun tallafin N50,000
Sai dai akwai sharadi ga masu cin gajiyar shirin, inda SMEDAN ta bayyana cewa duk wanda ya samu tallafin dole ne ya dauki akalla mutum daya aiki domin karfafa samar da guraben aikin yi.
Hukumar ta ce ta kirkiro shirin ne domin saukaka wa kananan 'yan kasuwa samun tallafin kudi, musamman wadanda ke fuskantar matsalar samun rancen kasuwanci daga cibiyoyin kudi.
A cewar SMEDAN, shirin zai kuma taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci, kara yawan masu sana'o'i da habaka tattalin arziki a matakin kananan hukumomi.
Hukumar ta bayyana cewa wannan shirin ya bambanta da Presidential Conditional Grant Scheme, duk da cewa dukkansu na bayar da tallafin N50,000 ga kananan sana'o'i.
Abubuwan da ake bukata
Masu neman tallafin za su cike bayanai kamar:
- Cikakken suna
- Adireshin imel
- Lambar waya
- Sunan kasuwanci
- Lambar rajistar CAC (idan akwai)
- Nau'in kasuwanci
- Tsawon shekarun da aka yi ana gudanar da kasuwancin
An shawarci masu neman tallafin da su tabbatar da cewa duk bayanan da suka bayar daidai ne.
Abubuwan da za a iya amfani da kudin
Masu cin gajiyar shirin na iya amfani da kudin wajen:
- Siyan kayan aiki
- Kara jarin kasuwanci
- Inganta fasahar gudanar da kasuwanci
- Fadada harkokin kasuwanci
- Horo da bunkasa kwarewa
- Shiga sabbin kasuwanni

Source: Getty Images
Yadda ake neman tallafin
SMEDAN ta bukaci masu sha'awar shirin su yi amfani da shafin yanar gizo da aka bude domin masu neman tallafin, kamar yadda Punch ta rahoto.
Ana kuma shawartar masu neman tallafin su cike fom din neman tallafin cikin tsanaki tare da tabbatar da cewa sun cika dukkan sharudan shiga shirin kafin su mika bukatarsu.
An bude shafin rancen wayoyi da kwamfuta
Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta buɗe shafin neman bashin samun komfuta, wayoyin hannu da na'urorin zamani ga 'yan Najeriya.
An kaddamar da shirin a ranar Talata, wanda CREDICORP ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar ma'aikatar sadarwa a birnin tarayya Abuja.
A yanzu haka an fara shirin gwaji ne da wadanda suka shiga shirin 3MTT su 1,000 kafin a faɗaɗa shi zuwa ga sauran al'umma.
Asali: Legit.ng
