Babbar Magana: Atiku Ya Shiga Damuwa bayan Tura Kudi Masu Nauyi a Asusunsa

Babbar Magana: Atiku Ya Shiga Damuwa bayan Tura Kudi Masu Nauyi a Asusunsa

  • Atiku Abubakar ya ce an tura kudi zuwa daya daga cikin asusun ajiyarsa a banki daga mutumin da bai sani ba
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bai nemi gudunmawar ba, bai amince da ita ba, kuma bai san wanda ya aika kudin ba
  • Ya ce lamarin ya tayar da tambayoyi kan tsaron bayanan bankunan 'yan Najeriya da yiwuwar amfani da su ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan wasu kudi da aka tura masa.

Atiku ya nuna damuwar ne kan wani abin da ya kira shigar masa da kudi cikin yanayi mai cike da shakku zuwa daya daga cikin asusun ajiyarsa na banko da ke wani babban bankin kasuwanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya yi maganar sulhu da 'yan bindiga bayan ya je ta'aziyya

An turawa Atiku kudi a asusunsa na banki
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a shafinsa na X ranar Juma'a, 7 ga watan Agustan 2026.

A cewar sanarwar, an turo kudin ne daga wani mutum da Atiku ya ce bai sani ba, tare da bayanin cewa: "gudunmawa domin yakin neman zabe".

Sanarwar ta ce Atiku ko tawagarsa ba su nemi wannan gudunmawa ba, ba su ba da izini a aika ta ba, kuma ba su da masaniya kan mutumin ko kungiyar da ta tura kudin.

Atiku ya nuna damuwa kan tsaron bayanan banki

Atiku ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda aka samu bayanan asusun ajiyarsa na sirri, duk da cewa ba a bayyana su ga jama'a ba.

Sanarwar ta ce:

"Asusun bankin na sirri ne kacokan, kuma bayanansa ba su ga jama'a. Wannan ya haifar da tambaya mai muhimmanci: Ta yaya wasu da ba a san ko su waye ba suka samu bayanan sirrin bankin wani mutum?"

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun budewa jama'a wuta

Ta kara da cewa idan har ana iya samun bayanan bankin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, hakan na nuna cewa sirrin bayanan bankin kowane dan Najeriya na iya kasancewa cikin hadari.

Ya bukaci a yi bincike

Atiku ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne zargin cewa watakila an samu wadannan bayanai ne ta hannun wasu masu damar samun sirrin bayanan banki.

Ya ce idan aka tabbatar da hakan, zai zama babban cin zarafin iko wanda zai iya jefa mai asusun cikin hadarin masu garkuwa da mutane, 'yan ta'adda, 'yan bindiga, masu damfara da sauran masu aikata laifuka.

Sanarwar ta ce an sanar da al'ummar Najeriya da hukumomin tsaro game da wannan lamari, wanda ta bayyana a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke haifar da shakku gabanin babban zaben shekara mai zuwa.

"Ba za su dauke mana hankali Ba"

Atiku ya ce yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi, bai kamata 'yan Najeriya su bari irin wadannan dabaru su dauke musu hankali ba.

Ya bayyana lamarin a matsayin wata hanya ta bata suna, yana mai cewa irin wadannan dabaru sun taba gazawa a baya kuma za su sake shan kunya.

Kara karanta wannan

Dalilan EFCC na garkame asusun gwamnatin Osun kafin zabe

Sanarwar ta kammala da cewa Waziri Adamawa na ci gaba da mayar da hankali wajen gabatar wa 'yan Najeriya ingantaccen shugabanci da mafita ga kalubalen da kasar ke fuskanta.

Atiku ya jefo tambayoyi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Facebook

Atiku ya kalubalanci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya kalubalanci Shugaba Tinubu da ya umarci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka (ICPC) ta saki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng