'Yan Ta'adda Sun Mayar da Yaran da Suka Sace cikin Kungiyarsu
- Yara 25 da ke cikin mutanen da aka sace a Kebbi, Kwara da Neja sun mutu a hannun ’yan ta’adda kuma aka binne su a cikin daji
- Mutane 315 sun samu ’yancinsu bayan shafe watanni shida a hannun ’yan ta’adda, yayin da wasu 12 suka shiga rundunar ’yan ta’addan
- Mata biyu da aka sace suna da ciki sun dawo da jarirai biyu, bayan ’yan uwansu sun ce masu garkuwar ba su taba su ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Ilorin, jihar Kwara – Yara 25 da ke cikin mutane 336 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihohin Kebbi, Kwara da Neja sun mutu a hannun masu garkuwar, inda aka binne su a cikin daji.
Hon. Saidu Baba-Ahmed, ɗan majalisar wakiltar mazabar Gwanabe/Gweria/Bani/Adena ta ƙaramar hukumar Kaiama a majalisar dokokin jihar Kwara, ne ya bayyana hakan jiya.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Source: Original
Baba-Ahmed ya shaida wa jaridaranguard cewa matasa 12 sun shiga rundunar ’yan ta’addan, don haka ba sa cikin mutanen da aka saki.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin da mutane 315 da aka sace suke ciki, bayan da ’yan ta’addan suka sake su a daren Alhamis bayan shafe watanni shida a hannunsu.
Adadin ya ƙunshi mutane 308 da aka ceto daga hannun ’yan ta’adda a dazukan jihohin Kwara da Neja, da kuma ɗalibai bakwai na Gateway ICT Polytechnic da ke Saapade a jihar Ogun, waɗanda aka sace a makon da ya gabata.
Wasu matasa sun shiga rundunar ’yan ta’adda
"’Yan ta’addan sun tambayi matasan wane ne a cikinsu yake son shiga rundunarsu, sannan 12 daga cikinsu suka ba da kansu. Don haka, waɗannan matasan ba sa cikin wadanda aka saki."
“Yara 25 daga Kebbi, Neja da Kwara su ma sun mutu a hannun ’yan ta’addan, yayin da wasu suka mutu a hanya. An binne su a can."
“Mutane 176 aka sace daga jihar Kwara, amma 163 ne suka samu ’yancinsu. Mutane 15 daga cikinsu har yanzu ba a san inda suke ba.” In ji shi.
Mata biyu sun dawo da jarirai
Dan majalisar ya kuma bayyana cewa babu wata daga cikin matan da aka saki da ta dawo da ciki, sai dai mata biyu da aka sace suna da ciki sun dawo da jarirai biyu.
Ya ce an binciki matan sosai kuma aka tabbatar da cewa babu wadda take da ciki, domin sun bayyana cewa masu garkuwar ba su taba su ba.
An kai wadanda aka saki Ilorin
Hon. Saidu Baba-Ahmed ya ce mutanen da aka saki sun isa Ilorin, babban birnin jihar Kwara, inda ake duba lafiyar 46 daga cikinsu a asibiti.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kwara ce ke kula da mutanen domin tabbatar da halin lafiyarsu kafin a mayar da su ga iyalansu.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun yi barazana
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi barazanar aurar da kyawawa daga cikin matan da suka sace daga jihar Kwara.
'Yan bindigan sun yi barazanar aurar da matan da suke ganin suna da kyau tare da kashe sauran mutanen da suke riƙe da su.
Asali: Legit.ng
