‘Suna Saduwa da Matansu’: Tsohon Gwamna kan Yadda Rashin Wuta ke Kara Yawan Mutane
- Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki a Karkara, Ayodele Fayose, ya ce rashin wutar lantarki na sa mutane zama gida da daddare
- Fayose ya ce rashin wuraren nishaɗi bayan dare ya yi na sa mutane komawa gida da wuri, lamarin da ya danganta da karuwar haihuwa
- Ya ce samar da ingantacciyar wutar lantarki zai bunkasa harkokin dare da nishaɗi, tare da rage yawan mutanen da ke zama gida da daddare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ekiti - Tsohon gwamnan Ekiti kuma shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara, Ayodele Fayose, ya yi magana kan illar wutar lantarki ba.
Fayose ya danganta karuwar yawan jama’ar Najeriya da rashin wutar lantarki, yana mai cewa rashin ingantaccen wutar lantarki na tilasta wa mutane zama a cikin gida da dare.

Source: Facebook
Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Arise News da su ka yi a Abuja a ranar Juma'a 7 ga watan Agustan shekarar 2026.
Fayose ya danganta rashin wuta da yawan mutane
Ya ce rashin wutar lantarki na takaita harkokin dare da sauran nau’o’in nishaɗi, lamarin da ke barin mutane da ‘yan hanyoyin da za su bi da yamma.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa a samu hanyoyin yadda za a ingata wutar lantarki a fadin kasar saboda inganta harkokin kasuwanci da masana'antu.
Ya ce:
“Me ya sa ba ku magance wannan matsalar wutar lantarki ba? Mutanen da ke wannan matakin ba su da wani abin nishaɗi na daban. Babu wani abu da ya fi muhimmanci a gare su. Bayan ƙarfe 7 na dare, duhu ya mamaye wurin.”
A cewarsa, mutane kan zaɓi zama a gida tare da kwanciya barci da wuri saboda ƙarancin wuraren nishaɗi bayan duhu ya shiga.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Source: Facebook
Yadda rashin wuta ke hada mata da maza
Ya ce mutane na kusantar matansu saboda rashin wutar da za ta debe masu kewa su yi hira ko wani abu mai muhimmanci game da ci gaban rayuwarsu.
Ya ƙara da cewa:
“Kowa yana kusantar matarsa. Kuma yawan jama’a kawai sai ya ninka. Matsalar kawai ita ce rashin wutar lantarki.”
Fayose ya ce inganta samar da wutar lantarki zai sauya yadda mutane ke gudanar da lokutan yamma, ta hanyar samar da damar gudanar da harkokin dare da sauran ayyuka.
“Tun a tunaninsu sun riga sun yanke cewa, to, idan wannan ne kaɗai abin nishaɗin da ake da shi, bari in zauna a nan. Amma idan muka magance matsalar wutar lantarki, za a samu harkokin dare."
- Cewar Fayose
Mulkin Tinubu ya fi na Buhari
An ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ce halin da ake ciki a gwamnatin Bola Tinubu ya fi lokacin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan
Halin da wutar lantarki ke ciki bayan narka kuɗi sama da Naira tiriliyan 10 a Najeriya
Babban 'dan adawar wanda ya dawo APC yana yabon gwamnatin Tinubu ne a lokacin da wasu ke rade-radin zai iya sauya sheka zuwa APC mai-ci.
Fayose ya ce yabon gwamnatin APC ba shi da nasaba da batun sauya sheka, domin ba zai taba rabuwa da PDP ba.
Asali: Legit.ng
