Bincike kan Shirin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki Ya Rutsa da Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya

Bincike kan Shirin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki Ya Rutsa da Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya

  • An zargi fitaccen jarumin Nollywood, Stanley Amandi, da amincewa da aikin shirya farfaganda domin tallafa wa wadanda suka shirya juyin mulki
  • Bincike ya ce an bukaci ya tsara yadda za a tara jama'a da kuma shirya bukukuwan nuna goyon baya a jihohin Kudu maso Gabas
  • Amandi ya shaida wa masu bincike cewa ya karɓi N100,000 daga wani jami'in soja bayan wata ganawa a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani fitaccen jarumin Nollywood, Stanley Amandi, wanda ya shahara wajen taka rawa a fina-finai, ya tsinci kansa a cikin binciken da ake yi kan yunkurin juyin mulki a Najeriya.

Masu bincike kan lamarin sun tatsi bayanai daga jarumin kan abin da ya shafi zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ma'aji.
Wanda ake zargi da jagorantar shirin juyin mulki a Najeriya, Kanal Mohammed Ma'aji Hoto: DHQ Nigeria
Source: Twitter

Bincike ya kai kan jarumin Nollywood

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya shiga damuwa bayan tura kudi masu yawa a asusunsa

Bayanan bincike da Premium Times ta samu sun nuna cewa Amandi, ya amince da wani aiki na tsara yadda za a shirya farfaganda da neman goyon bayan jama'a a Kudu maso Gabas idan shirin juyin mulkin ya yi nasara.

A cikin bayaninsa ga masu bincike, jarumin ya bayyana yadda wata abota da wani soja ta fara cikin sauki, kafin daga bisani ta rikide zuwa tattaunawa kan yiwuwar sauya gwamnatin Najeriya da karfin bindiga.

A cewar bayaninsa, Amandi bai taba tunanin cewa wata ganawa ta bazata bayan wani taron horas da matasa masu shirya fina-finai a Enugu za ta kai shi cikin binciken daya daga cikin manyan zarge-zargen laifuka a Najeriya ba.

Yada sojan Najeriya ya jawo jarumi Amandi

Ya ce ya fara haduwa da wani soja mai mukamin Warrant Officer, Nas a wani taron masu shirya fina-finai da aka gudanar a Newberries Park da ke National Museum, Enugu.

Ya ce duk da cewa a baya ba ya jin dadin alakarsu, amma sojan ya samu amincewarsa, har ya rika gayyatarsa zuwa barikin soja da ke Enugu.

A cewarsa, ziyarar ta kara yawa, inda aka rika maraba da shi, aka gabatar da shi ga wasu jami'ai, har ya fara jin kamar barikin gidansa ne.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Trump ya fadi wanda ya ke so ya gaje shi a Amurka

An ba shi aikin Kudu maso Gabas

A cewar bayaninsa, an bukaci Amandi da ya tsara yadda za a samu goyon bayan jama'a a Kudu maso Gabas nan take bayan kifar da gwamnati Tinubu.

Amandi ya ce an bukaci ya koma Enugu ya tsara yadda za a gudanar da wannan gangamin a jihohin Kudu maso Gabas biyar tare da shirya kasafin kudin da ake bukata.

Ya ce daga bisani an tsara kasafin kusan N50 miliyan domin gudanar da ayyukan a jihohin Kudu maso Gabas biyar.

Amandi.
Fitaccen jarumi a masana'antar Nollywoo, Stanley Amandi Hoto: Stanley Amandi
Source: Facebook

Jarumi Amandi ya karbi N100,000

Ya ce kusan mako guda bayan ya dawo daga taron, wannan soja ya tuntube shi ya ce Ma'aji ya yaba masa saboda halartar gayyatar.

A cewarsa, ya tura bayanan asusun bankinsa kamar yadda aka bukata, sannan ya samu N100,000. Ya ce nan take ya aika wa Ma'aji sakon godiya kan kudin.

A lokacin bincike, ya ce ya yi tunanin kai rahoton abin da ya sani ga hukumomi, sai dai ya ce wata magana da sojan ya yi masa ta sa ya ji tsoron bayyana abin da ya sani.

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba

Juyin mulki: Yadda Ma'aji ya sayi motoci

Kun ji cewa wani dillalin motoci ya shaida wa masu bincike cewa Kanal Mohammed Ma’aji ya sayi motoci shida kan Naira miliyan 65

Ana zargin an sayi motocin ne a watan Satumban 2025, lokacin da ake kyautata zaton masu shirin juyin mulki sun tsananta shirye-shiryensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262