Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe
Gombe - Isa Ali Ibrahim Pantami ya gamu da kalubale iri-iri tun daga lokacin da ayyana burinsa na neman takarar gwamna a jihar Gombe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Da fari wasu sun fara nuna cewa a matsayinsa na malamin addinin Musulunci, Isa Ali Ibrahim Pantami bai dace ya shiga harkar siyasa ba.
Legit Hausa ta kawo rahoto da ya dauko wahalhalun da ‘dan takaran na PDP ya fuskanta a hanyarsa ta ganin ya zama gwamnan Gombe a 2027.
Kalubalen da takarar Isa Pantami ta samu
1. Cire shi daga cikin ‘ya ‘yan APC
Tun farko an zargi Isa Pantami da cewa ya yi watsi da APC a jihar Gombe duk da damar da jam’iyyar ba shi na zama shugaban NITDA da ministan tarayya.
Isa Ali Pantami ya kare kan shi, yana bayanin dalilin da ya sa ya ja baya daga siyasar Gombe a lokacin da Gwamna Inuwa Yahaya yake tsakiyar mulki.

Kara karanta wannan
Atiku: Dino Melaye ya bada labarin yadda kotu ta kira lauyoyin ADC karfe 11:00 na dare
Bayan tuhumar kin taimakon jam’iyya, Pantami ya yi raddi ga masu yi masa kallon bako a siyasa, a nan ya shaida cewa su ne sojojin boye tun zamanin CPC.
2. Rashin samun goyon baya a jam’iyyar APC
Jam’iyyar APC ta reshen jihar Gombe ta zabi ta fitar da ‘yan takara ta hanyar sasanci maimakon a shirya zaben tsaida gwani na kato-bayan-kato.
A sanadiyyar haka aka zabi Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin wanda ake so ya zama ‘dan takarar gwamna, Isa Ali Pantami bai amince da wannan ba.
Ganin haka Sheikh Isa Pantami ya ce APC ba ta cika sharadin sasanci ba don haka ya bukaci a shirya wa masu neman takara zaben tsaida gwani.
3. Isa Pantami ya bar jam’iyyar APC
Bayan ya bukaci a shirya zaben fitar da gwani na gaskiya sai kuma aka ji ya soki tsarin, yana mai nuna cewa jam’iyyar APC ba ta shirya yin adalci ba.
Saboda haka sai aka ji ya sanar da ficewarsa daga APC amma duk da haka jam’iyyar ta gudanar da zabe, kuma ta ce yana cikin wadanda suka shiga.
A zaben tsaida gwanin da aka yi, an ce malamin da ministan sufuri sun zo bayan Jamilu Gwamna.
4. Shigarsa jam’iyyar PDP
Kwatsam bayan ya sanar da duniya ya rabu da APC, sai aka fara jin Farfesa Isa Pantami zai shigo PDP, kuma haka aka yi a cikin watan Mayun 2026.
Sai dai ya shigo PDP ne a lokacin da manyan ‘yan siyasa irinsu Khamisu Mailantarki suke ciki kuma sun ci burin samun takarar gwamna a zaben badi.
A lokacin nan aka rika tuna wa malamin Musuluncin bakaken addu’o’in da ya yi wa PDP a baya.
5. PDP: Nasarar Pantami ta bar baya da kura
A ranar 26 ga watan Mayu 2026 aka tabbatar da cewa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin ne zai yi wa jam’iyyar PDP takarar gwamna.
Duk da PDP ta ce Sheikh Isa Pantami ya samu kuri’u 52, 955 a fadin jihar Gombe, abokon karawarsu a PDP ba su yi na’am da wannan matsaya ba.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru, Amaechi ya fito da yadda suka yi da Buhari kan wanda yake so ya gaje shi a 2023
Irinsu Usman Aliyu Garry da Khamisu Ahmed Mailantarki sun shigar da kara a kotu, suna kukan cewa PDP ba ta bi ka’ida wajen tsaida ‘dan takara ba.
6. Kotu ta soke tikitin da PDP ta bada
Idan ba a manta ba, wani kalubale da Pantami ya ci karo da shi kuma shi ne soke zaben tsaida gwanin da jam’iyyar PDP ta shirya a reshen jihar Gombe.
A Satumban 2026 kotun tarayya ta yi hukunci game da karar da aka yi dangane da kasancewar Pantami ‘dan jam’iyya da kebe wasu masu neman takara.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ta umarci jam’iyyar adawar ta sake gudanar da zaben tsaida gwani, amma kotu ba ta hana malamin shiga takara ba.
7. Sabon zaben tsaida gwani a PDP
Ganin an ba jam’iyya kwanaki 30 ta shirya sabon zabe na tsaida gwani, dole PDP ta yi maza ta sake yin wani zaben a ranar 29 ga watan Satumba 2026.
Wannan karo Isa Pantami ya buga da Khamisu Mailantarki da Aliyu Usman Garry a zaben kato-bayan-kato a duka kananan hukumomi 11 na jihar Gombe.
An ji Pantami ya samu kuri’u 2,054 sai Mailantarki ya tashi da 389 yayin da Garry ya samu 112.
8. Babu sunan Pantami a INEC
Duk da haka, da hukumar INEC ta tashi wallafa sunayen wadanda za su yi takara a jihohi a zaben 2027, sai aka nemi sunan tsohon ministan tarayyan aka rasa.
Baya ga rashin sunan shi, a shafin INEC an nuna PDP ba ta ma da ‘dan takaran gwamna a Gombe.
Hukumar zaben ta fake da cewa ta yi haka ne saboda yin biyayya ga hukuncin Kotun koli dangane da shari’ar da aka yi a kan dokar zabe ta shekarar 2026.
9. Lauyoyi sun shigar da korafi
Saboda abin da ya faru, ‘dan siyasar ya dauko hayar lauyoyi a karkashin jagorancin Ahmed Raji SAN, yana kalubalantar INEC ta saka sunan sa cikin masu takara.
Lauyoyin sun ba INEC wa’adin kwanaki uku, amma har lokacin ya wuce ba a ga sunan shi ba.
Ahmed Raji SAN ya kare zaben tsaida gwani da jam’iyyar PDP ta yi, yana cewa babu yadda za a iya cire sunan farfesan ba tare da wani umarni daga wajen alkali ba.
10. INEC ta wallafa sunan Pantami
Duk da hukumar INEC ta wallafa sunan Sheikh Pantami a karshe cikin ‘yan takaran Gombe, akwai sauran rina a kaba domin kuwa shari’a ba ta kare a kotu ba.
Jami’in hukumar, Mohammed Haruna ya ce an karbi korafin da aka shigar bayan an yi nazari.
Sai dai Mohammed Haruna ya nanata cewa takararsa ta dogara ne da hukuncin karshe da kotu ta yi, lamarin da ya kusa yin kama da halin NDC a jihar Kano.
Asali: Legit.ng


