Yadda Sanata Ta Fadi yayin Kamfen APC Wanda Ya Yi Sanadiyar Rayuwarta

Yadda Sanata Ta Fadi yayin Kamfen APC Wanda Ya Yi Sanadiyar Rayuwarta

  • Sanatare Idiat Adebule ta rasu ne bayan ta faɗi a yayin gudanar da kamfen ɗin APC a mazaɓarta
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an garzaya da ita asibitin Duchess International da ke Ikeja, amma ta cika kafin a samu nasarar ceto ta
  • Shugaba Bola Tinubu, Godswill Akpabio, Barau Jibrin, Sanwo-Olu da sauran manyan 'yan siyasa sun yi alhinin rasuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - Sabbin bayanai sun bayyana kan yadda Sanata mai wakiltar Lagos ta Yamma, Idiat Adebule, ta rasu a ranar Asabar.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayiyar ta rasu ne kwana ɗaya bayan bikin cikarta shekaru 56 a duniya.

An yi rashin sanata a Lagos
Sanata mai wakailtar Legas ta Yamma a Majalisar Dattawa, Dr. Idiat Adebule Hoto: Ayoade Ojeniyi.
Source: Twitter

Yadda Sanata Idiat ta rasu a Lagos

Wata majiya daga jam’iyyar APC a Lagos ta shaida wa jaridar Punch cewa marigayiyar ta faɗi ne yayin gudanar da ayyukan kamfen a mazaɓarta.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi a Najeriya, Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar sanata

Majiyar ta ce an garzaya da ita wani asibiti mai zaman kansa da ke yankin GRA, Ikeja, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarta.

Ta bayyana cewa:

“Ta faɗi ne yayin kamfen a mazaɓarta. An kai ta asibiti, amma ba a samu nasarar ceto ta ba. Abin takaici ne, rana ce mai cike da baƙin ciki a gare mu.”

Wata majiya mai tushe kuma ta bayyana cewa marigayiyar ta jima tana fama da rashin lafiya, inda ta kasance tana ƙoƙarin kula da lafiyarta.

Majiyar ta ƙara da cewa tana fama da wata cuta da ba a bayyana sunanta ba, kuma an gan ta kwanaki kaɗan kafin rasuwarta yayin kamfen gida-gida na APC a garin FESTAC.

Ta ce bayan faɗuwarta a ranar Asabar, an garzaya da ita asibitin Duchess International da ke Ikeja, inda ta rasa hayyacinta kafin daga bisani ta rasu.

Sanata Adebule, wadda ke neman komawa majalisar dattawa karo na biyu, ta yi bikin cikarta shekaru 56 a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Sanatar APC ta riga mu gidan gaskiya bayan bikin cikarta shekaru 56

Sanata ta fadi a yayin kamfen APC
Taswirar jihar Lagos da aka yi rashin sanatar APC. Hoto: Legit.
Source: Original

APC ta magantu kan rasuwar sanata Idiat

Jam’iyyar APC ta tabbatar da rasuwarta ta cikin wata sanarwa da kakakinta na Lagos, Seye Oladejo, ya sanya wa hannu, cewar Vanguard.

A cikin sanarwar, jam’iyyar ta bayyana dakatar da dukkan ayyukan kamfen da take gudanarwa a faɗin jihar saboda rasuwar sanatar.

Oladejo ya kuma sanar da cewa za a yi jana'izar marigayiyar a ranar Lahadi, 29 ga Nuwamba, a makabartar Ebony Vaults and Gardens da ke Ikoyi, Lagos, da ƙarfe 3:00 na rana.

Ya ce rasuwar Adebule babban rashi ne ga jam’iyyar APC da kuma iyalan siyasar Lagos, yana mai cewa gudunmawar da ta bayar wajen mulki da ci gaban jihar ba za a manta da ita ba.

Tinubu ya yi jimamin rasuwar sanata

Mun ba ku labarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sanata kuma tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos.

Sanatar mai shekaru 56 ta rasu ne a Lagos bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya jefa iyalanta da abokan siyasarta cikin alhini.

Tinubu ya bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga Lagos da Najeriya, inda ya yaba da gudummawar da ta bayar a harkokin gwamnati da ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.