Fusatattun Matasa Sun Lalata Fastocin Tinubu, Wike bayan Hari kan Taron Yan APC

Fusatattun Matasa Sun Lalata Fastocin Tinubu, Wike bayan Hari kan Taron Yan APC

  • Mahara sun kai hari a wurin taron haɗakar ƙungiyoyin Rainbow Coalition a Imo, inda suka ƙona allunan tallata Tinubu da Wike
  • Maharan sun kuma ƙona tantuna, kujeru, janareto da wasu kayayyaki, tare da jikkata mutane da dama yayin da suke ƙoƙarin tserewa
  • Duk da harin, Sanata Samuel Anyanwu ya bukaci magoya bayan ƙungiyar su halarci taron da aka shirya gudanarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Wasu ’yan daba sun kai hari a wurin da aka shirya gudanar da taron haɗakar ƙungiyoyin Rainbow Coalition.

An shirya taron ne domin nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu da kuma duk yan APC a Najeriya.

An kai hari a taron APC da aka shirya a Imo
Allunan hotunan Bola Tinubu da Nyesom Wike da aka lalata a Imo. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Lamarin ya faru ne ranar Asabar a makarantar Central da ke Amaimo, ƙaramar hukumar Ikeduru, kwana guda kafin gudanar da taron ranar Lahadi, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

An kai hari a taron goyon bayan Tinubu

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ikenna Onuoha, mai ba Samuel Anyanwu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce maharan sun ƙona kayayyaki da dama.

Onuoha ya bayyana cewa harin ya faru ne yayin da masu shirya taron ke aikin kafa dandamali da tantuna domin gudanar da gangamin siyasar.

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun samu raunuka yayin da suke ƙoƙarin tserewa domin tsira da rayukansu daga harin.

A cewarsa, maharan sun kutsa wurin taron ne a lokacin da ake shirya shi, inda suka buɗe wuta tare da cinna wa kayayyaki da kadarori wuta.

Haka kuma, ya ce maharan sun ƙona allunan talla, fastoci da sauran kayayyakin kamfen da ke ɗauke da hotunan Tinubu da Nyesom Wike.

Wike shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja, kuma sanarwar ta yi zargin cewa maharan sun yi wa wasu mutane duka tare da amfani da bindigogi da sauran muggan makamai.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yan bindiga sun tashi gari, sun banka wa gidaje da shaguna wuta

An kona allunan Wike da Tinubu a Imo
Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike da ke goyon bayansa. Hoto: Lere Olayinka, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

An shawarci magoyan bayan Tinubu, Wike

Duk da harin, Anyanwu ya buƙaci mambobi da magoya bayan Rainbow Coalition da ke Imo su halarci taron da aka shirya gudanarwa a Amaimo.

Ya ce ba za a fasa gangamin ba duk da abin da ya kira yunƙurin tayar da hankali da kawo cikas ga taron.

Sanarwar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro, fadar shugaban ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga lamarin domin hana sake samun tashin hankali.

Ta buƙaci hukumomin su ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa harkokin siyasa na gudana cikin kwanciyar hankali a jihar, cewar Punch.

Wike ya daga wa gwamnonin APC hankali

An ji cewa gamayyar Rainbow Coalition ta Nyesom Wike na haifar da rikici a APC a jihohin Imo, Kwara da kuma Gombe gabanin zaɓen 2027.

Ministan ya dage ƙungiyar za ta taimaka wa Bola Tinubu ya sake lashe zaɓe, amma za ta iya goyon bayan ’yan takarar PDP a wasu zaɓukan.

Duka gwamnonin da suke yaƙar gamayyar Rainbow Coalition sun fito neman takaran kujerun Majalisar dattawa a ƙarƙashin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.