Minaj: Mawakiyar Amurka Ta Tuna Najeriya a Lamuranta, Ta Yi Mata Addu’a

Minaj: Mawakiyar Amurka Ta Tuna Najeriya a Lamuranta, Ta Yi Mata Addu’a

  • Shahararriyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj, ta aika da saƙon addu’a ga Najeriya bayan kisan magoya bayan NDC
  • Peter Obi ya ce an kashe mambobin jam’iyyarsa huɗu a harin siyasa, inda ya ziyarci waɗanda suka jikkata tare da iyalan mamacin
  • Rundunar ’yan sandan Delta ta tabbatar da mutuwar mutane shida, yayin da ta fara bincike tare da kama wasu da ake zargi da hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Shahararriyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj, ta nuna goyon baya ga Najeriya bayan hare-hare a jihar Delta.

Minaj ta mayar da martani kan saƙon Peter Obi game da kisan wasu magoya bayan jam’iyyar NDC mai adawa a Delta.

Nicki Minaj ta yi wa Najeriya addu'a
Mawakiya Nicki Minaj da dan takarar shugaban kasa, Peter Obi. Hoto: @NICKIMINAJ, @PeterObi.
Source: Twitter

Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, ya wallafa sanarwa a shafinsa na X ranar Asabar, inda ya yi Allah-wadai da harin.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun lalata fastocin Tinubu, Wike bayan hari kan taron yan APC

Martanin Obi kan kisan yan NDC

Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana cewa ya samu labarin kisan mambobin jam’iyyarsa huɗu a ranar 23 ga Nuwamba, lokacin da yake gudanar da tarukan tattaunawa da al’umma a jihohin Neja da Nasarawa.

Ya ce bayan samun labarin, ya dakatar da saƙonnin siyasa na yau da kullum domin mayar da hankali kan ta’aziyya da kira ga zaman lafiya.

Obi ya bayyana cewa daga bisani ya ziyarci waɗanda suka jikkata da ke karɓar magani a asibitocin Capital Hospital da Lily Hospital a Warri.

Haka kuma, ya ziyarci iyalan marigayi Umokoro Efemena Kelly, tare da nuna alhini a madadin jam’iyyar da ’yan takararta na gwamna da sanata a Delta.

A cikin sanarwarsa, Obi ya ce:

“Bayan waɗannan munanan abubuwan da suka faru, na yanke shawarar dakatar da duk saƙonnin siyasa da rubuce-rubucen da nake wallafawa, sai dai saƙonnin ta’aziyya da kira ga zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Siyasa ta yi zafi: Takarar Obi da Kwankwaso ta ci karo da gagarumar matsala

“A irin wannan lokaci mai cike da baƙin ciki, na ga ya dace a bai wa iyalan mamatan damar jimamin rashinsu, a tausaya wa waɗanda suka jikkata, sannan a yi tunani kan rashin rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
“Abin damuwa ne matuƙa yadda shiga harkokin siyasa da ’yancin zaɓen wanda mutum yake so ke ƙara jefa ’yan Najeriya cikin barazana, tashin hankali, har ma da rasa rayukansu."
Obi ya koka an kisan yan NDC
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: UGC

Martanin da Nicki Minaj ta yi

A ranar Lahadi ne Nicki Minaj ta mayar da martani ga saƙon Obi a shafinsa na X, inda ta wallafa alamomin addu’a da tutar Najeriya.

Wannan martani nata ya ja hankalin mutane sosai, inda cikin ’yan sa’o’i kaɗan ya samu dubban mutane da suka nuna goyon baya tare da yaɗa shi.

Ana son Obi ya janyewa Tinubu takara

An ji cewa Shugaban Hukumar Bincike da Bunƙasa Albarkatun Ƙasa (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ike-Muonso, ya bukaci Peter Obi ya janye takararsa ta shugaban ƙasa a 2027.

Ike-Muonso ya kuma bukaci ’yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu domin ya samu damar ci gaba da aiwatar da manufofinsa na tattalin arziki.

A wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar ya ce ya kamata Kudancin Najeriya ya kammala wa’adin mulkin shekara takwas kafin a mayar da mulki Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.