ADC Ta Kwance wa Shettima Zani a Kasuwa kan Tasirinsa a Wurin Tinubu
- Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa matar Shugaba Tinubu, Remi; dansa Seyi da wasu manyan jami'ai sun fi Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima tasiri
- ADC ta bayyana Shettima a matsayin mai tallata kamfen Tinubu, wanda ba shi da abin da zai kare game da nasarorin gwamnatin APC
- Jam'iyyar ta kalubalanci mataimakin shugaban ƙasar da ya yi bayani kan tsadar kayan abinci, sufuri da wutar lantarki a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam'iyyar adawa ta ADC ta yi ikirarin cewa wasu manyan mutane a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun fi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tasiri da karɓuwa.
ADC ta ambaci matar shugaban ƙasar, Sanata Remi Tinubu; ɗansa, Seyi; shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da Ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin mutanen da suka fi Shettima tasiri.

Source: Facebook
ADC ta dura kan Kashim Shettima
Jam'iyyar ta bayyana Shettima a matsayin wanda aka mayar tamkar mai tallata kamfen Tinubu, wanda ba shi da ƙarfin kare manufofi da nasarorin gwamnatin tarayya, cewar Arise TV.
Wannan martani na ADC na zuwa ne bayan da Shettima ya yi magana a wajen gangamin kamfen jam'iyyar APC da aka gudanar a Enugu ranar Asabar.
A yayin gangamin, mataimakin shugaban ƙasar ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, zai koma garinsu Yola da ke jihar Adamawa bayan zaɓen 2027.
Da yake mayar da martani cikin fushi, daraktan yaɗa manufofin sadarwa na kwamitin kamfen shugaban ƙasa na ADC, Phrank Shuaib, ya yi tambayar yadda Shettima zai yi barazanar yin ritaya da wani mutum alhali shi kansa ba shi da wani tasiri.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, Shuaib ya ce tun lokacin da aka zaɓi Shettima a matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa, siyasar tasa ta fara yin kama da ta wanda ya yi ritaya.
Ya zargi mataimakin shugaban ƙasar da rage aikinsa zuwa halartar gangamin APC domin yi wa Atiku ba'a, amma ya ɓace idan 'yan Najeriya suka nemi ya yi bayani kan tsadar abinci, sufuri da wutar lantarki.
Shuaib ya ce Shettima ya kwashe shekaru uku da rabi yana shiru kan matsin tattalin arzikin da gwamnatin da yake cikinta ta jefa 'yan Najeriya, amma yanzu an dawo da shi fagen siyasa saboda zaɓe na gabatowa.
Ya ƙara da cewa kalaman da Shettima ya yi kan yawan wuraren da Atiku ke kai kamfen ba su da zurfi, domin bai kamata a mayar da su tamkar nazarin siyasa ba.
Daraktan ya bayyana cewa idan za a auna tasirin jami'an gwamnatin Tinubu bisa ga yadda ake sauraron su, maimakon muƙamansu na kundin tsarin mulki, Shettima zai sha wahala wajen shiga cikin manyan mutane biyar.
Shettima ya dura kan Atiku
An ji cewa Kashim Shettima ya ce yana da damar sukar Atiku Abubakar saboda wasan da yake tsakanin Bare-bari da Fulani.
Ya ce Peter Obi, Seyi Makinde, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi duk abokansa ne duk da bambancin siyasarsu.
Shettima ya bukaci ’yan Najeriya su sake zaɓen Bola Tinubu a 2027, yana mai kare manufofin tattalin arzikinsa.
Asali: Legit.ng

