A Karshe, INEC Ta Wallafa Sunan Pantami cikin 'Yan Takarar Gwamna a 2027

A Karshe, INEC Ta Wallafa Sunan Pantami cikin 'Yan Takarar Gwamna a 2027

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta saka sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar Gombe na zaben 2027
  • A shafin hukumar da Legit Hausa ta duba a safiyar ranar Asabar, an ga sunan Pantami tare da Haruna Ahmad a matsayin mataimakinsa
  • Pantami ne dan takara na 15 cikin mutum 19 da za su fafata a zaben gwamnan Gombe da za a gudanar a watan Fabrairun 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta saka sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin jerin sunayen ’yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne bayan rahotannin da suka nuna cewa an maido da sunan shi cikin 'yan takara a wannan makon.

Kara karanta wannan

Yadda aka ceto malaman da aka sace za su tafi yi wa Tinubu addu'a a Zamfara

Sheikh Is aAli Pantami na wa'azi
Dan takarar PDP a Gombe, Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano sunan tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani a shafin hukumar zaben da safiyar ranar Asabar, inda aka jera shi tare da Haruna Ahmad a matsayin wanda zai yi masa mataimaki.

Pantami na cikin ’yan takara 19

Bayanan da ke shafin INEC sun nuna cewa Pantami shi ne na 15 cikin ’yan takara 19 da za su fafata domin neman kujerar gwamnan jihar Gombe.

Zaben gwamnan na daga cikin zabukan da hukumar INEC za ta gudanar a watan Fabrairun 2027.

Bayanin da aka samu a shafin hukumar ya fayyace cewa a karkashin jam’iyyar PDP Pantami zai yi takarar gwamna a 2027.

Martanin Sanata Dankwambo

Mai magana da yawun jagoran PDP a Gombe Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya tabbatar da cewa an maido sunan Pantami cikin 'yan takara.

Hadimin Sanata Dankwambo kan harkokin yaɗa labarai, Hussaini Ali Muhammed ya wallafa a shafin PDP na Gombe na Facebook cewa:

Kara karanta wannan

Hanyoyin da INEC za ta bi ta magance tashin hankali a zaben 2027

"A ƙarshe, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sabunta shafinta na yanar gizo, inda ta saka sunan Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP na kujerar gwamnan jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027."

Ya kara da cewa:

"Haka kuma, hukumar ta saka sunan Hon. Hassan Adamu Haruna (Danmasanin Waja), a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna daga ƙaramar hukumar Balanga."

Ya yi godiya ga Allah da cewa:

"Alhamdulillahi! Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa baiwar nasarar da Ya ba mu.
"Muna matuƙar godiya gare Shi bisa ni’imominSa, kuma muna roƙonSa da Ya ba mu nasara a babban zaɓen shekarar 2027, kamar yadda Ya ba mu nasara a wannan mataki, ta rahamarSa da ikonSa marar iyaka."
Sheikh Pantami a wajen taron PDP
Dan takarar PDP a Gombe, Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Bayanin Jamilu Gwamna

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar APC, Jamilu Gwamna, ya bukaci ’yan jam’iyyar su kara himma wajen tallata shi a tsakanin al’umma.

A wani bayani da ya yi, Jamilu Gwamna ya ce duk wanda ya gaza kawo akwatin mazabarsa ba zai kasance tare da shi ba bayan kafa gwamnati.

Ya kuma bukaci mambobin APC su tabbatar sun samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’u sama da miliyan daya a zaben da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng