INEC Ta Yi Magana kan Hukuncin Kotun Koli da Ake Ganin Ya Shafi Takarar Sheikh Pantami
- Hukumar INEC ta ce za ta fara nazarin kwafin hukuncin Kotun Koli kafin ta yanke shawarar yadda za ta aiwatar da shi
- Wasu ‘yan takara da aka ce hukuncin zai iya shafar burinsu a zaben 2027 sun dage cewa hukuncin bai shafe su ba
- Hukuncin Kotun Koli ya dawo da wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026 da suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu da hanyoyin tsayar da ‘yan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta fara duba Kwafin Hukunci na Gaskiya (CTC) d Kotun Koli ta yanke kwanan nan kan wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026 da ake takaddama a kansu.
INEC ta bayyana cewa za ta yi nazarin wannan hukunci kafin ta dauki matsaya kan yadda za ta aiwatar da shi.

Kara karanta wannan
Hukuncin kotun ƙoli ya hana Sheikh Pantami neman takarar gwamna a PDP? Bayanai sun fito

Source: Facebook
Mataimakin Daraktan INEC mai kula da wayar da kan masu kada kuri’a da yaɗa labarai, Wilfred Ifogah, ne ya bayyana hakan jiya yayin da yake amsa tambayar jaridar Leadership kan tasirin hukuncin.
Hakan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan takara da ake ganin cewa takarar da suka samu na iya kasancewa cikin hadari sakamakon hukuncin Kotun Koli suka dage cewa hukuncin bai shafe su ba.
Daga cikinsu akwai tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya kuma ɗan takarar gwamnan Nasarawa na SDP, Mohammed Abubakar Adamu; tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani kuma mai neman takara a PDP, Farfesa Isa Ali Pantami.
INEC za ta yi nazari kan hukuncin kotu
Sai dai Ifogah ya ce hukumar zaɓen za ta fara karɓar Kwafin Hukunci (CTC), kafin ta gudanar da zama domin nazarin abin da ke cikin hukuncin tare da yanke shawarar matakin da za ta ɗauka.
Ya ce:
“Dole ne hukumar INEC ta yi zama bayan ta karɓi Kwafin Hukunci (CTC). Idan kuna tambayata ra’ayina kan hukuncin, ina ganin ba ni da wani abin cewa, amma ina ganin hukumar za ta yi zama ta nazarce shi, sannan ta yanke shawara.”
Hukuncin d Kotun Koli ta yanke
Kotun Koli ta amince da korafin INEC kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ranar 16 ga Yuli, wanda ya soke wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026 da suka shafi rajistar mambobin jam’iyyun siyasa da tsayar da ‘yan takara.
Kotun koli ta hannun kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Adamu Jauro, ta soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da dawo da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Takaddamar ta samo asali ne daga ƙarar da ZLP ta shigar a Babbar Kotun Tarayya, inda ta kalubalanci Sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na Dokar Zabe ta 2026.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa waɗannan tanade-tanade sun saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, sannan kuma suna katsalandan ne cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.

Source: Facebook
Babbar Kotun Tarayya, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Umar, ta yi watsi da ƙarar a ranar 5 ga Mayu, 2026, lamarin da ya sa ZLP ta ɗaukaka ƙara.
Daga bisani, Kotun Ɗaukaka Ƙara ya amince da ɗaukaka ƙarar a wani ɓangare a hukuncin da ta yanke ranar 16 ga Yuli, tare da soke tanade-tanaden da ake takaddama a kansu.
Saboda rashin gamsuwa da hukuncin, INEC ta garzaya Kotun Koli tana neman a dawo da waɗannan tanade-tanade, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Daga bisani Kotun Koli ta dage yanke hukunci bayan ta saurari hujjojin ɓangarorin a ranar 16 ga Satumba, kafin ta yanke hukuncin a ranar 24 ga Satumba.
Kungiyar Pantmiyya ta yi martani
Kun ji cewa magoya bayan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami sun ce hukuncin Kotun Koli ba zai hana dan takararsu neman kujerar gwamnan Gombe a 2027 ba.
Pantamiyya ta bayyana cewa hukuncin bai hana Pantami shiga wani sabon zaben fidda gwani na PDP ba, tana mai cewa ikirarin cewa an cire Pantami daga takarar yaudara ne.
Asali: Legit.ng

