Tinubu Ya Wulakanta Atiku, Obi da Sauran Masu Kalubalantar Shi a 2027
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas su zabi dukkan 'yan takarar APC a 2027
- Tinubu ya sanar da amincewa da gina layin dogo na Gabas da bututun iskar gas mai tsawon kilomita 400
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce al’ummar Igbo za su yi asara idan suka ki mara wa Tinubu da APC baya a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci al’ummar jihar Enugu su kada kuri’a ga dukkan 'yan takarar jam’iyyar APC a babban zaben 2027.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da yakin neman zaben APC a jihar, inda ya yi ikirarin cewa jam’iyyun adawa ba su da wani tasiri a kasar.

Source: Twitter
Shugaban ya bukaci mazauna jihar su karbi katin zabe na dindindin (PVC), sannan su karfafa wa abokansu da 'yan uwansu gwiwa su zabi APC, cewar Punch.
Tasirin APC a yankin Kudu maso Gabas
Ya kuma yi ikirarin cewa manyan 'yan siyasa a Kudu maso Gabas suna tare da shi kuma suna goyon bayan jam’iyyar APC.
Tinubu ya bukaci masu zabe su marawa jam’iyyar baya a zaben shugaban kasa, na majalisar dokoki ta kasa da sauran mukamai.
Ya ce:
“Kada ku bari wani ya yaudare ku. Sauran jam’iyyun ba su wanzu, ba su da tsare-tsare kuma ba su san hanyar da za su bi ba.
“Na ga Orji Kalu a nan, na ga dan uwana daga Imo yana tattara mutane domin APC. Na ga babban mutum a nan, Arthur Eze, hamshakin dan kasuwa ne amma mai goyon bayan APC. Yana son alamar tsintsiya.
“Dan uwana, tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, shi ma yana tare da ni. Me kuma kuke bukata? Mataimakin shugaban majalisar wakilai ma yana nan. Dan uwanku yana tare da ku, muna sanye da kaya iri daya kuma muna jam’iyya daya."

Source: Facebook
Ayyukan da Tinubu ya yi a yankin
A yayin taron, Tinubu ya sanar da amincewa da aikin gina layin dogo na Gabas da kuma bututun iskar gas mai tsawon kilomita 400 domin yankin Kudu maso Gabas.
Ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin alkawuran gaskiya da gwamnatinsa ta dauka, wadanda za a tabbatar da aiwatar da su.
Shugaban ya ce layin dogon Gabas zai hada yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu da kuma Arewacin Najeriya.
A cewarsa, aikin zai taimaka wajen magance korafe-korafen da ake yi na cewa an ware yankin daga manyan ayyukan layin dogo na kasa.
Tinubu ya kuma yi alkawarin kara tallafa wa manoma ta hanyar basussuka marasa ruwa, taimakon kudi da samar da ababen more rayuwa domin rage musu nauyin noma.
Shettima ya bukaci Igbo su goyi bayan Tinubu
An ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce yankin Kudu maso Gabas na da abubuwa da dama da zai amfana da su idan ya hada kai da jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura wa Atiku saƙo bayan cika shekaru 80, ya tuna halaccin da ya yi masa
Shettima ya bukaci al’ummar yankin su karfafa alakar da suke da ita da jam’iyyar, yana mai cewa ba za su iya yin watsi da hadin kai da shugaba Tinubu ba.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma yi wa 'yan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, da Peter Obi na NDC shagube.
Asali: Legit.ng

