Kishi Ya Tashi: Patience Ta Yi Magana kan Amaryar Jonathan da Ta Bayyana

Kishi Ya Tashi: Patience Ta Yi Magana kan Amaryar Jonathan da Ta Bayyana

  • Patience Jonathan ta yi magana kan zargin auren tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da wata mata, inda ta tambayi ko doka ta amince da auren mace biyu a kotu
  • Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa ta yi tambayar ne yayin wata hira da aka yi da ita bayan an tambaye ta game da Ayima Lott-Jonathan
  • Kalaman nata sun zo ne kwanaki bayan Ayima ta ƙaddamar da littafinta mai suna Gold Dust: Treasures of Quiet Years a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Patience Jonathan, tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar Najeriya kuma matar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ta yi magana kan zargin mijinta ya sake aure.

Patience ta nuna shakku kan yiwuwar mutum ya yi aure da mata biyu a ƙarƙashin tsarin auren kotu, tana mai cewa kotu ba ta amince da hakan ba.

Kara karanta wannan

Sanata ya yi magana kan saƙon 'yan sanda bayan an yi yunƙurin kashe shi a wurin kamfe

Matar Jonathan ta yi magana kan amaryarsa
Tsohon shugaban asa, Goodluck Jonathan da matarsa Patience. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

An tambayi Patience game da Ayima Lott-Jonathan, wadda ake zargin ita ce matar Goodluck Jonathan ta biyu, yayin wata hira da gidan talabijin na NTA da aka wallafa a YouTube.

Patience ya magantu kan amaryar Jonathan

A yayin hirar, Patience ta tambayi mai gabatar da shirin ko doka ta amince mutum ya auri mata biyu a ƙarƙashin tsarin auren kotu lamarin da ya jawo tambayoyi kan batun.

Ta ce:

“Ban san abin da kike magana a kai ba. Da farko dai, a kotu, mutum zai iya auren mata biyu?”

Mai tambayarta ya amsa da cewa a'a, inda Patience ta mayar da martani da cewa:

“To, ka yanke hukunci da kanka.”

Wannan bayani nata ya fito ne kwanaki kaɗan bayan Ayima Lott-Jonathan ta ƙaddamar da littafinta mai suna Gold Dust: Treasures of Quiet Years a wani taro da aka gudanar a Abuja.

An ƙaddamar da littafin ne a ranar 19 ga Nuwamba, 2026, kuma taron ya zo daidai da bikin cikar Ayima shekaru 50 a duniya.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Wata babbar mota ta bi ta kan uwa da ƴarta a Abuja za su tallaka titi

Yadda Patience ta zama 'First Lady' a Najeriya

Ƙaddamar da littafin ya ba ta damar bayyana wasu abubuwa game da rayuwarta da abubuwan da ta fuskanta, bayan ta shafe tsawon lokaci ba ta cika fitowa fili ba a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Patience Jonathan ta kasance uwargidan shugaban ƙasar Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, bayan mijinta ya zama shugaban ƙasa sakamakon rasuwar tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.

Kafin hakan, ta riƙe matsayin uwargidan gwamnan Bayelsa daga shekarar 2005 zuwa 2007, lokacin da mijinta ke jagorantar jihar a matsayin gwamna.

Dalilin Jonathan na mika mulki cikin sauki

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da ya sa ya miƙa mulki ga Muhammadu Buhari cikin lumana.

Jonathan ya bayyana hakan ne ta bakin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim, yayin bikin ƙaddamar da tarihin rayuwar Buhari a Abuja.

Kashim Shettima ya yaba wa Buhari, yana mai cewa halayensa sun nuna cewa mutuncin shugabanci yana dogara ne da nagartar wanda ke riƙe da muƙamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.