Ficewar Pantami daga APC Ta Bar Baya da Kura, Jam'iyyar Ta Fitar da Sabon Bayani

Ficewar Pantami daga APC Ta Bar Baya da Kura, Jam'iyyar Ta Fitar da Sabon Bayani

  • A kwanakin baya tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP
  • Jam'iyyar APC ta fito ta bayyana cewa tsohon Ministan sadarwar bai yi murabus daga cikinta kuma har yanzu mambanta ne
  • Ta kuma yi magana kan batun cewa Farfesa Pantami, ya samu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu kan burinsa na yin takarar gwamna a inuwar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ta jaddada cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Ali Pantami, yana nan a matsayin mambanta.

APC ta dogara da cewa ba a bi hanyoyin da suka dace ba game da murabus ɗinsa daga zama mamban jam'iyyar.

APC ta ce Pantami bai bar cikinta ba
Farfesa Isa Ali Pantami a wajen taro Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa sakataren yada labarai na jam'iyyar, Moses Kyari, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

NDC ta yi martani kan batun Kwankwaso ya yi barazanar barin jam'iyyar

Wannan ƙarin haske yana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin cewa Pantami ya zama ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Gombe bayan ya fafata a zaɓen fitar da gwaninta.

APC ta ce Isa Pantami mambanta ne

Moses Kyari ya ce kwamitin zartarwa na mazaɓar jam'iyyar bai amsa ko tattaunawa kan kowace wasiƙar murabus da aka danganta da tsohon Ministan ba, rahoton Daily Post ya nuna hakan.

Kyari ya bayyana cewa mutane 25 daga cikin mambobi 27 na kwamitin zartarwa na mazaɓar sun fito fili sun yi watsi da iƙirarin murabus ɗin, inda suka bayyana shi da na ƙanzon kurege kuma wanda ba a karba ba.

Ya ce shugabancin mazaɓar ya jaddada cewa babu wani tsari na murabus na hukuma da aka kammala daidai da tsarin mulkin APC, Dokar Zaɓe, ko kuma ƙa'idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Shin APC ta karbi wasikar Pantami ta murabus?

A cewarsa, shugaban APC a mzaɓar, Alhaji Bala Galda, ya tabbatar da cewa wasiƙar murabus ɗin da ake zargin ta Pantami ce na dauke da kwanan watan ranar 19 ga watan Mayu, 2026, amma an amshe ta a ranar 23 ga watan Mayu, ta hannun wani wakili da aka bayyana sunansa da Abba Pantami.

Kara karanta wannan

'Dan takarar gwamnan Bauchi zai gamu da cikas da PDP ta taso shi a gaba

Kyari ya ƙara da zargin cewa ba a taɓa ba shugabannin mazaɓar damar duba takardar da ake magana a kai ba, wanda hakan ya haifar da shakku kan ingancinta da kuma halaccin tsarinta.

Mai magana da yawun jam'iyyar ya jaddada cewa a ƙarƙashin doka, Pantami yana nan a matsayin mamban APC har sai an tantance tare da kammala dukkan matakan da ake buƙata na yin murabus yadda ya kamata.

APC ta tayar da kura kan Pantami
Farfesa Isa Ali Pantami zaune a ofis Hoto: Prof Isa Ali Pantami
Source: Twitter

Batun Pantami ya samu goyon bayan Tinubu

Ya kuma yi watsi da iƙirarin da aka jinginawa Pantami wanda ke nuna cewa komawarsa PDP da kuma burinsa na tsayawa takarar gwamna suna da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Sakataren yada labaran ya bayyana iƙirarin a matsayin wanda ba gaskiya a cikinsa, kuma bai dace da kishin da shugaban kasar yake yi wa jam'iyyar APC ba.

Ya yi kira ga shugabancin APC na ƙasa da kuma fadar shugaban kasa da su fito fili su yi bayani kan wannan batu domin hana yaɗuwar labaran ƙarya da kuma bayyana matsayin jam'iyyar ga jama'a.

Pantami ya samu goyon baya a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, ya samu goyon baya a siyasar jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai kan ficewar Sheikh Pantami daga jam'iyyar APC a Gombe

Dr. Ibrahim Adamu Usman, wanda ya nemi takarar kujerar Sanata na Gombe ta Arewa a jam’iyyar LP, ya sanar da ficewarsa daga cikinta tare da goyon bayan takarar Pantami.

Tsohon ɗan takarar Sanatan ya bayyana Pantami a matsayin babban malami da ƙwararren masani a harkokin tsaron yanar gizo, fasaha kuma jagoran sauye-sauyen zamani a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng