Rikicin NDC: Jam'iyyar Su Kwankwaso Ta Kori Dan Takarar Sanata a Zaben 2027

Rikicin NDC: Jam'iyyar Su Kwankwaso Ta Kori Dan Takarar Sanata a Zaben 2027

  • Jam’iyyar NDC a Jihar Kwara ta kori ɗan takararta na sanatan Kwara ta Tsakiya, Dakta AbdulRasheed Suleiman Omoda
  • Jam’iyyar ta zarge shi da yin watsi da takararsa tare da nuna goyon baya ga Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq
  • Omoda ya tabbatar da goyon bayansa ga gwamnan, amma ya ce har yanzu bai yi murabus a hukumance daga NDC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Jam’iyyar NDC a Jihar Kwara ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na sanata, Dakta AbdulRasheed Suleiman Omoda, bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa muradun jam’iyyar.

Ta sanar da korar tasa ranar Asabar, tana zargin ɗan takararta na kujerar Sanatan Kwara ta Tsakiya da yin watsi da burinsa na neman kujerar, tare da nuna goyon baya ga Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Tutar NDC.
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya, NDC Hoto: NDC
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, ta ce kwamitin gudanarwarta na jiha ne ya yanke matakin a wani taro na musamman da ya kira bayan Omoda ya bayyana a bainar jama’a cewa zai janye daga takarar sanatan tare da mara wa gwamnan baya.

Kara karanta wannan

Awanni 24 bayan bikin cika shekaru 56, Allah ya yi wa sanatar APC rasuwa

NDC ta kori dan takarar Sanata

Sakataren NDC na jiha, Eyitayo Adedamola ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Ilorin.

Ya ce kwamitin ya ɗauki matakin ne bayan neman izini da samun amincewar shugabancin NDC na ƙasa, bisa tanadin Mataki na 19 na kundin tsarin mulkinta.

Adeogun ya ce shugabancin jam’iyyar na ƙasa ya bayar da izini a rubuce ga kwamitin NDC ta Kwara domin amfani da ikonsa na ladabtarwa da kuma korar Omoda bisa yanayin da ake ciki.

Dalilin korar Omoda daga NDC

Ya ce:

“Dr. Omoda ya ƙi miƙa wasiƙar janyewa daga takara a hukumance. Idan mutum ya amince da tikitin takarar jam’iyyarmu, hakan na ɗora masa nauyin mambobin da suka ba shi amanar.
“Idan ya yanke shawarar janyewa, muna sa ran zai sanar da mu hakan a hukumance tare da bin tsarin janyewa daga takara.”

Ya kuma bayyana cewa wani tsohon babban jami’in gwamnatin Jihar Kwara ya nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar Sanatan Kwara ta Tsakiya a ƙarƙashin inuwar NDC.

Kara karanta wannan

Sanata ya yi magana kan saƙon 'yan sanda bayan an yi yunƙurin kashe shi a wurin kamfe

Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta bi ƙa’idojin zaɓe da suka dace wajen duba wannan batu.

Omoda ya mayar da martani

Sai dai da yake magana da jaridar Daily Trust, Omoda, wanda ya tabbatar da shawarar da ya yanke ta mara wa gwamnan baya, ya ce har yanzu bai yi murabus daga NDC a hukumance ba.

Omoda ya bayyana cewa yana “jiran umarni daga shugabancin jam’iyyar na ƙasa kan wane daga cikin shugabannin ɓangarorin biyu na jam’iyyar da ke Jihar Kwara zai miƙa wa wasiƙar murabus ɗinsa”.

NDC ta shirya ceto Najeriya

Kun ji cewa jam’iyyar NDC ta yi alƙawarin ceto ’yan Najeriya daga ƙalubalen tattalin arziki da rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso , ne ya fadi hakan, inda ya zargi gwamnatin APC maiNmulki da gaza wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262