Mailantarki: Abokin Hamayyar Pantami Ya Zo da Sabon Batun kan Zaben Fitar da Gwanin PDP
- Khamisu Mailantarki ya ce an ɗauki kalamansa ba daidai bayan rahotannin da suka ce ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwanin PDP
- Mailantarki, wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 389, ya ce ya kamata a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara bisa yanayin shari’ar kotu
- Ya ƙalubalanci cancantar Isa Pantami, yana mai cewa zai garzaya kotu kan shigarsa zaɓen fitar da gwani na PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Ɗaya daga cikin masu neman tikitin gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Khamisu Mailantarki, ya ce bai taɓa ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe sabon zaɓen fitar da gwamni na jam’iyyar ba.
Mailantarki ya ce ba shi da ikon ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, yana mai cewa an ɗauki kalamansa ba daidai ba wata hira da ya yi bayan kammala zaɓen.

Source: Facebook
Khamisu Mailantarki wanda ya shiga zaben fitar da gwanin ya bayyana hakan ne yayin wata wata tattaunawa da jaridar The Punch.
Mailantarki ya ce rahotannin da suka ce ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwanin na ranar Talata, 29 ga watan Satumban 2026 ba su bayyana abin da ya faɗa daidai ba.
"Na karanta kanun labarai da dama da suka ce na ayyana kaina a matsayin wanda ya lashe sabon zaɓen fitar da gwamni na ranar Talata."
“Ba zan iya yin hakan ba saboda ba ni da ikon yin hakan. An ɗauke ni abin da na fada ba daidai ba a taron manema labarai na bayan zaɓen.” In ji shi.
Mailantarki ya zo na biyu da ƙuri’u 389
Mailantarki ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwamni da aka gudanar ranar Talata, inda ya samu ƙuri’u 389.
Sai dai ya ce waɗannan su ne halastattun ƙuri’un da aka kada masa a matsayinsa na ɗan jam’iyyar PDP mai rajista.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
A cewarsa, adadin ƙuri’un da ya samu ya isa ya ba shi damar zama wanda ya yi nasara, saboda ɗan takarar da ya biyo bayansa ya samu ƙasa da nasa ƙuri’un.
Ya ƙalubalanci cancantar Pantami
Mailantarki ya nuna rashin amincewarsa da cancantar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, na shiga sabon zaɓen fitar da gwanin.
Ya dage cewa bai kamata a bari Pantami ya shiga zaɓen ba, yana mai cewa bai cika ƙa’idojin jam’iyyar na zama ɗan jam’iyya ba kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani na farko.
Ya ce zai kai batun kotu
Mailantarki ya yi nuni da wani hukunci na baya-bayan nan da Kotun Ƙoli ta yanke kan wani batu makamancin wannan, yana mai cewa zai ƙalubalanci Pantami a kotu.
Ya ce kundin tsarin mulki da sauran dokokin ƙasar sun ba shi damar ƙalubalantar lamarin.
A cewarsa, batun cancantar Pantami bai samu cikakkiyar mafita ba, kuma wannan na daga cikin dalilan da suka sa ya yanke shawarar neman kotu ta shiga lamarin.
Mailantarki ya ce duk da cewa an gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani bisa ƙa’idojin da aka shimfiɗa, shigar Pantami cikin takarar ta sanya sakamakon zaɓen ya kasance abin da za a iya ƙalubalanta.
Ya yabawa shugabannin PDP na Gombe
A gefe guda, Mailantarki ya yaba wa shugabancin PDP a Jihar Gombe kan yadda suka gudanar da harkokin jam’iyyar.
Musamman ya yaba wa tsohon gwamnan jihar kuma Sanata, Ibrahim Hassan Dankwambo, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin tabbatar da adalci da bin ƙa’idoji a harkokin jam’iyyar.

Source: Facebook
PDP ta dakatar da Mailantarki
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta reshen Jihar Gombe ta dakatar da Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki da Hon. Usman Aliyu Garry. W
Matakin dakatarwar ya biyo bayan zarginsu da aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyyar.
Asali: Legit.ng

