Atiku: Dino Melaye Ya Bada Labarin Yadda Kotu ta Kira Lauyoyin ADC Karfe 11:00 na Dare
- Dino Melaye ya ce kimanin karfe 11:00 na dare aka sanar da lauyoyinsu cewa za a yanke hukunci a shari’ar shugabancin ADC
- Tsohon sanatan na jihar Kogi yana ganin akwai tufka da warwara a hukuncin alkalin don haka yake ganin tamkar ba a yi ba ne
- Da yake kamfe a Birnin Kebbi, Sanata Dino yake cewa APC ta tsorata ne da mutanen da suka tarbi Atiku Abubakar a Sokoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kebbi - Dino Melaye ya cigaba da rura wuta a yakin siyasar da ake bugawa tsakanin ‘yan jam’iyyar APC da kuma na ADC mai hamayya.
Tsohon sanatan na Kogi ta yamma ya yi tir da yadda alkali ya yi hukuncin da ya taba takarar shugaban kasar Atiku Abubakar a ADC a 2027.

Source: Facebook
Dino Melaye ya soki hukuncin kotu a shari'ar ADC
A wani bidiyo da shi kan shi Dino Melaye ya daura a Facebook, an ji yana bayanin abin da ya jawo kotu ta yi hukuncin da ya kawo masu cikas.
Sanata Dino ya alakanta hukuncin kotun tarayyan da taron mutanen da aka gani sun halarci gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar ya bude kamfen a jam’iyyar ADC a garin Sokoto, wanda ya ha hankalin mutane sosai.
Da yake magana a Kebbi, ‘dan siyasar ya ce tururuwan mutanen da aka gani suna goyon bayan Atiku ya sa aka yi gaggawar yanke hukunci.
Jawabin Dino Melaye a taron kamfen ADC
‘Dan siyasar ya ce cikin dare da karfe 11:00, kotun tarayyar ta sanar da su lauyoyinsu su hallara a Abuja domin alkali zai yi hukunci da safe.
Ya ce:
“Bayan Tambuwal ya yi masu wata shegiyar allura a Sokoto, sai suka firgita. Karfe 11:00 na dare aka kira lauyoyinmu aka ce masu yau za a yi hukunci.
Karfe 11:00 na dare, idan ba maye ba…ai lokacin mayu suke taro kenan. Amma kar ku ji komai, doka ta ce idan kotu ta bada umarni, sai wata kotun kamar ta, ta bada wani umarnin, to wanda ya fara bada umarni shi za a bi.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi
Kuma alkali Liman ya ce, wasikar da Ralph Nwosu ya rubuta masa yana sanar da shi su David Mark yana cikin ka’ida, doka ba ta hana ba. Saboda haka ta yadda da David Mark. Duk wata karya da ta biyo baya ba labari ba ne?
Sanata Dino ya zargi 'yan sanda da kai masu hari
Baya ga maganar kotu, Daily Post ta rahoto shi yana cewa kafin su iya zuwa wurin kamfe, sai da ‘yan sanda sama da 100 suka tare su a kan hanya.
Dino ya zargi jami’an tsaron da jifansu da duwatsu tare da kuma watsa masu borkonon tsohuwa.
A nan ya tuna masu cewa shugaban ADC na kasa wato David Mark mutum ne da ya kai kusan matsayin janar a lokacin da yake aiki a gidan soja.
Haka zalika ya ce shi ma Atiku Abubakar wanda yake tike da tutar shugaban kasa a jam’iyyar ya samu horon ‘dan sanda tun da yake aikin kwastam.
Wahalar da ADC ta sha wajen kamfe a Sokoto
Gwamnatin Sokoto ta ki ba Atiku Abubakar wurin taro, ana zargin an hana ‘yan ADC samun otal lokacin da suka zo yawon yakin neman zabe.
Rahoto ya ce mahukanta da ke karkashin APC sun yi wa masu babura umani su kaurace wa tituna saboda a hana ‘yan adawa zirga-zirga a jihar.
Kashim Ibrahim Imam ya bada labarin irin hanyoyin da suka bi domin ganin an tallata Atiku a Sokoto.
Asali: Legit.ng

