Zamfara: Dan Takarar Sanata Ya Sha da Kyar a Kamfen APC, an Samu Raunuka
- An yi arangama a wajen gangamin APC a Shinkafi, inda aka raunata magoya bayan jam’iyyar da dama
- An ce Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, mai neman kujerar sanatan Zamfara ta Arewa, ya tsira daga wani yunƙurin kashe shi
- Shinkafi ya kai ziyara asibiti ga waɗanda suka jikkata, inda ya ba kowannensu Naira 100,000 domin taimaka musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Shinkafi, Zamfara - An samu tashin hankali a wajen gangamin kamfen ɗin shugaban ƙasa da na gwamnan APC a jihar Zamfara.
An tabbatar da cewa lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda aka raunata magoya bayan jam’iyyar da dama.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya ce rikicin ya faru ne a ranar 27 ga watan Nuwamban 2026, inda wasu daga cikin waɗanda suka jikkata suka garzaya asibiti domin samun kulawar likitoci.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Sanatar APC ta riga mu gidan gaskiya bayan bikin cikarta shekaru 56
An kuma ruwaito cewa Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, wanda ke neman kujerar sanatan Zamfara ta Arewa, ya tsallake wani yunƙurin kashe shi da ake zargin an yi a lokacin rikicin.
Ƙungiyar Wannan Shinkafi Democratic Front ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa magoya bayan APC da dama sun samu munanan raunuka sakamakon tashin hankalin.
Sanarwar ta ce an kai waɗanda suka jikkata babban asibitin Shinkafi, inda suke karɓar magani bayan faruwar lamarin.
Bayan haka, Shinkafi ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibitin, inda ya ba kowannensu tallafin Naira 100,000 domin taimaka musu wajen biyan kuɗin magani.
Haka kuma, ya bayar da Naira 20,000 ga sauran marasa lafiyar da ke kwance a asibitin domin neman lafiya, cewar rahoton Punch.
Ƙungiyar ta yaba masa kan wannan ziyara da tallafin kuɗin da ya bayar, tana mai cewa hakan ya nuna damuwarsa kan halin da waɗanda abin ya shafa suke ciki.
Sai dai ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda tashin hankalin ya kawo cikas ga gangamin kamfen ɗin, inda ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike.

Kara karanta wannan
Sanata ya yi magana kan saƙon 'yan sanda bayan an yi yunƙurin kashe shi a wurin kamfe
Ta kuma yi kira da a tabbatar an hukunta duk waɗanda aka samu da hannu wajen haddasa rikicin, tare da ƙarfafa zaman lafiya a jihar.
Haka kuma, ta shawarci ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyu daban-daban da su rungumi siyasa cikin lumana, tare da kauce wa duk wani mataki da zai ƙara rura wutar rikici a Zamfara.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng