Takarar Pantami Ta Samu Matsala, Kotu Ta Soke Zaben Fitar da Gwanin PDP
- Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a jihar
- Usman Aliyu Garry ne ya shigar da ƙara yana kalubalantar zaman Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam'iyyar PDP
- Kotun ta ce dole PDP ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da dokokin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta umarci Jam’iyyar PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a Jihar Gombe.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar.

Source: Facebook
A cikin karar, Usman Aliyu Garrya ya kalubalanci zaman Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
2027: Bayan hukuncin kotu, PDP ta ɗauki matsaya kan takarar Sheikh Pantami a jihar Gombe
Aliyu Usman Garry ya ƙalubalanci zaman Pantami ne bayan da jam’iyyar ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni 2026.
Ya yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani da ya dace ba kafin sanar da Farfesa Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Pantami ya koma PDP daga APC
Kafin komawarsa PDP, Pantami ya kasance ɗaya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Sai dai bayan APC ta amince da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na maslaha, Pantami ya fice daga jam’iyyar ya koma PDP.
Daga bisani, an tabbatar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP yayin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayun 2026.
Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da zaɓen
A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, 24 ga watan Satumban 2026, kotun ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani domin zaɓen ɗan takarar gwamna a jihar.

Kara karanta wannan
Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira
Kotun ta ce sabon zaɓen dole ne ya kasance bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma dokokin da suka shafi gudanar da zaɓe, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Hukuncin ya zo ne yayin da siyasar Gombe ke ƙara samun sauye-sauye gabanin zaɓen gwamnan jihar.
Hukuncin kotun dai zama koma baya ga takarar Farfesa Isa Ali Pantami wanda ke neman zama gwamnan jihar Gombe a inuwar jam'iyyar PDP.
Farfesa Pantami dai na daga cikin 'yan takarar da ke kan gaba a neman kujerar gwamnan Gombe a zaben 2027.m

Source: Twitter
Jigon PDP ya caccaki Farfesa Pantami
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP kuma wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Gombe, Hon. Khamisu Ahmad Mailantarki ya yi magana kan siyasar Farfesa Isa Ali Pantami.
Hon Khamisu Ahmad Mailantarki ya bayyana rashin jin dadi kan yadda Farfesa Isa Ali Pantami ya yi masu rashin adalci.
Ya ce Farfesa Pantami ya bar layin malanta ya koma neman mabiya wadanda mafi yawansu ba ƴan Gombe ba ne domin haka ya kamata ya gyara siyasarsa.
Asali: Legit.ng