
Rikicin PDP







Bayan shiga ofis a matsayin shugaban rikon kwarya, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya bayyana kansa a matsayin dan yankin, yana mai sha'awar dawo da zaman lafiya.

Bayan Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, matashi dan PDP a Kaduna, Aliyu Kwarbai ya roki Sanata Ibrahim Khalid Soba kan dokar ta-ɓaci a Rivers

Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya roki 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga barazanar dokar ta-baci a Rivers.

Tsohon ɗan takarar majalisar dokokin Kano, Hon. Adnan Mukhtar Tuduk Wada ya soki shugaban matasan PDP na ƙasa, ya ce Muhammad Kadade ya gaza wakiltar matasa.

Dakataccen gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara ya tattara kayansa ya bar gidan gwamnati yayin da ake shirye-shiryen miƙa mulki ga sabon 'gwamnan riko'.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewa ta na kokarin tabbatar da mulkin danniya da murde 'yan adawa da ke fadin kasar nan.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa gwamnatin rikon kwarya a jihar Ribas jim kaɗan bayan sanar da dakatar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa.

Ministan Abuja, Wike ya kwace filin PDP a Abuja bisa gazawar jam’iyyar na biyan harajin filin tun 2006. FCTA ta ce ta sha jan kunne amma PDP ta ki biyan bashin.

Wasu membobin PDP sun bayyana takaicin yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ke yi wa jam'iyyar karan tsaye ta hanyar goyon bayan Tinubu ya yi nasara a zaben 2027.
Rikicin PDP
Samu kari