FBI Ta Sake Shigar da Bukata gaban Kotun Amurka kan Bayanan da Suka Shafi Tinubu

FBI Ta Sake Shigar da Bukata gaban Kotun Amurka kan Bayanan da Suka Shafi Tinubu

  • Hukumar FBI ta nemi ƙarin kwanaki 60 daga kotun Amurka domin bayyana dalilin da ya sa take ɓoye wasu bayanai da suka shafi Shugaba Bola Tinubu
  • Takardun sun shafi binciken da aka gudanar a farkon shekarun 1990 kan zargin safarar miyagun kwayoyi da kuɗaɗen haram da ake dangantawa da Tinubu
  • FBI ta ce tana da buƙatun neman bayanai 11,197 da ba ta kammala ba, tare da ƙarar da ake yi mata 534

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Washington DC - Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sake mika bukata ga kotun tarayya da ke Washington DC kan batun sakin bayanan da suka shafi shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Hukumar FBI ta nemi kotun ta ba ta ƙarin kwanaki 60 domin bayyana dalilin da ya sa take riƙe da wasu sassan takardun da suka shafi Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun lalata fastocin Tinubu, Wike bayan hari kan taron yan APC

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

FBI ta bukaci karin kwanaki 60

Leadership ta rahoto cewa FBI ta ce tana buƙatar ƙarin lokaci domin kwatanta takardun da ake takaddama a kansu da bayanan da jama’a za su iya samu daga cikin rahoton da take son ci gaba da ɓoyewa.

An bayyana buƙatar ne a cikin wata sanarwa mai kwanan watan 24 ga Nuwamba, 2026, wadda Melissa Corcoran, shugabar sashen yaɗa bayanan da takardun FBI, ta shigar.

An miƙa sanarwar ne a cikin ƙarar da wani ɗan rajin kare gaskiya da bayyana bayanai na Amurka, Aaron Greenspan, ya shigar a ƙarƙashin dokar ’yancin samun bayanai (FOIA) a Kotun Tarayya ta Gundumar Columbia.

Bayanan da ake neman FBI ta fitar

Ƙarar mai taken Greenspan v. Executive Office for U.S. Attorneys et al. (Civil Action No. 1:23-cv-01816-BAH), ta shafi neman samun takardun wani bincike da aka gudanar a farkon shekarun 1990 kan Shugaba Tinubu.

An yi binciken ne kan zargin safarar miyagun kwayoyi da kuɗaɗen haram da ake dangantawa da Tinubu, wadda aka ce ta samo asali daga Chicago.

Kara karanta wannan

"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

A cikin sanarwar, Corcoran ta ce FBI na buƙatar ƙarin lokaci domin bin umarnin kotu na ranar 30 ga Oktoba, 2026.

A cewar sanarwar da SaharaReporters ta samu, ta ce:

"FBI na neman kwanaki 60 domin gabatar da ƙarin sanarwa don tallafa wa sabon buƙatar waɗanda ake ƙara na neman hukuncin kotu ba tare da cikakken shari’a ba.”

Har yanzu kotun ba ta yanke hukunci kan buƙatar FBI ba.

Jami'an FBI.
Jami'an hukumar binciken manyan laifuffuka ta kasar Amurka (FBI) a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yawan ayyukan hukumar FBI

Domin bayyana dalilin da ya sa take buƙatar ƙarin lokaci, Corcoran ta yi nuni da yawan ayyukan sashen hukumar da ke kula da takardu, wanda ke gudanar da buƙatun neman bayanai ƙarƙashin dokar FOIA da kuma Dokar Kare Sirri (Privacy Act).

A cewar sanarwarta, sashen na da ƙwararrun ma’aikatan gwamnati 227 da ma'aukatan wucin gadi 93 da ke da alhakin nazarin takardu. A haɗe, suna duba shafukan takardu sama da miliyan 1.3 a duk shekara.

Abin da FBI take fargaba kan bayanan Tinubu

Kun ji cewa FBI ta nemi izinin kotun Amurka da ta gabatar mata da wasu bayanai a ɓoye kan dalilin da ya sa ta ƙi sakin wasu bayanan bincikenta da suka shafi zargin Bola Tinubu.

Hukumar ta ce bayyana wasu daga cikin bayanan zai iya tona asirin dabarun binciken jami'an tsaro tare da jefa rayuwar wasu mutane cikin haɗari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262