Pantami Ya Tara Manyan Lauyoyi Sun Tunkari INEC kan Cire Sunan Shi

Pantami Ya Tara Manyan Lauyoyi Sun Tunkari INEC kan Cire Sunan Shi

  • Luyoyin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da jam'iyyar PDP sun aikawa hukumar INEC wasiƙar neman a gaggauta saka sunansa a jerin ƙarshe na 'yan takarar gwamnan jihar Gombe na zaɓen 2027
  • Ahmed Raji (SAN) da sauran manyan lauyoyi sun bayyana cewa cire sunan Pantami daga jerin da INEC ta fitar ranar 10 ga Oktoba ba shi da tushe a shari'a saboda ya sake lashe zaɓen fitar da gwani
  • Lauyoyin sun ba hukumar INEC wa'adi zuwa Laraba, 14 ga Oktoba, 2026 domin ta sanya tare da yaɗa sunan Farfesa Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: APC ta samo alkaluman da suka nuna wanda zai ci zaben 2027

FCT, Abuja – Lauyoyin da ke wakiltar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, da jam'iyyar PDP sun shigar da buƙata ta gaggawa ga hukumar (INEC) kan cire sunansa daga jerin 'yan takarar gwamna a jihar Gombe.

Babban lauya Ahmed Raji (SAN), tare da haɗin gwiwar lauyoyi, sun aike da wasiƙa mai kwanan wata 12 ga Oktoba, 2026, zuwa ga Shugaban Hukumar INEC inda suka nuna rashin jin daɗinsu kan cire sunan Pantami ba tare da wani bayani na shari'a ba.

Dan takarar PDP, Sheikh Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a ofis. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Bukatar Pantami ga INEC

A cewar wasiƙar lauyoyin da aka wallafa a shafin dan takarar na Facebook, Pantami memba ne mai rajista a gundumar Pantami da ke jihar Gombe, kuma ya lashe zaɓen fitar da gwani na farko a ranar 26 ga Mayu, 2026.

Bayan shari’ar da aka yi a Babban Kotun Tarayya da ke Gombe, kotun ta rusa zaɓen sakamakon matsalolin gudanarwa amma ta wanke Pantami kan batun cancantar zama memba.

Lauyoyin sun jaddada cewa:

"Soke sunan ɗan takara aikin shari'a ne kawai a kotu, ba na INEC ba. Matsayin INEC shi ne halarta, lura, da gudanar da rahoto, ba soke ɗan takara ko zaɓen wanda take so ba."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya bayar da shawara ga Pantami da sauran 'yan takarar da INEC ta cire sunayensu

Pantami ya ba INEC kwana 3

Sakamakon haka, lauyoyin sun buƙaci hukumar INEC da ta tabbatar ta sanya sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin halattaccen ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin PDP kafin ko a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026.

Sun bayyana cewa suna sa ran INEC, a matsayinta na mai bin doka da umarnin kotu, za ta ɗauki matakin gyara cikin gaggawa kafin cikar wa'adin.

Shugaban hukumar INEC
Shugaban INEC a ofis. Hoto: INEC
Source: Facebook

'Yan takara sun tunkari INEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyun siyasa da 'yan takarar da aka cire sunayensu daga jerin ƙarshe na zaɓen gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da INEC ta fitar suna gudanar da baje kolin rashin amincewa.

Yayin da wasu jam'iyyu ke ganin kuskure ne na fasaha da ke buƙatar gyara tsakaninsu da INEC, wasu kuma sun alakanta shirin ɗaukar matakin shari'a domin dawo da sunayen 'yan takararsu kan jerin zaɓen na 2027.

Batun fitar da jerin sunayen ya shafi jam'iyyu daban-daban da suka haɗa da NDC, PDP, SDP da ADC a jihohi irin su Oyo, Gombe, Cross River, Benue da Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng