2027: Gwamna Abba ya samu tauhidi a batun koma wa mulkin jihar Kano

2027: Gwamna Abba ya samu tauhidi a batun koma wa mulkin jihar Kano

  • Abba Kabir Yusuf yana da burin sake tsayawa takara a 2027, amma bai ɗauki neman mulki a matsayin a mutu ko a yi rai ba
  • Ya jaddada cewa Allah ke ba da mulki kuma ya karɓa, yana mai cewa ya amince da shan kayen da ya yi a 2019 da nasarar 2023
  • Gwamnan Kano ya kuma umarci sababbin kwamishinoninsa da su inganta yaɗa labaran gwamnati kuma su yi gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana game da tazarce da yake hange domin cigaba da mulki har Mayun 2031.

Abba Kabir Yusuf yana neman zarcewa a ofis, mafi girman hamayyarsa za ta fito ne daga NDC da ta samu ‘yar matsala a dalilin kara a kotu.

Aminiya ta ce Abba Kabir ya bayyana cewa burinsa na sake tsayawa takarar gwamna a zaɓe mai zuwa ba maganar a mutu ko a yi rai ba ne.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Kamar yadda Kur’ani ya yi bayani, Gwamnan Kano ya bayyana cewa Allah SWT ne ke ba da mulki kuma yake karɓa a duk lokacin da ya so.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da yake rantsar da sababbin kwamishinoni da Majalisar Kano ta tantance a makon nan.

Abba Kabir ya nada kwamishinoni 2 a Kano

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya zama Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, sai Balarabe Sa’idu Gani ya zama Kwamishinan Ma’adinai.

A nan wurin Abba ya yi kira ga ‘yan siyasa cewa su bi a sannu wajen neman mulki domin Allah ne kaɗai ke ƙaddara wanda zai samu shugabanci.

Gwamnan ya tuno abin da ya faru a 2019 da aka ce an doke shi a takara da kuma kotun ƙararraki, sai ya rungumi ƙaddara har dama ta zo kan shi.

Babu zancen 'ko da tsiya-tsiya' wajen Abba

Mai girma gwamnan ya ce ya yi imanin cewa Allah ne ya ba shi nasara a zaɓen gwamnan Kano na 2023 bayan gwabzawa a takara da kuma kotu.

Abba ya rasa kujerarsa a Kotun sauraron ƙorafin zabe da kotun daukaka ƙara kafin alƙalan Kotun Ƙoli su yanke hukuncin da ya ba NNPP nasara.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fallasa danyen aikin da Buhari ya yi da ya bar Tinubu da wahala

A baya an saba jin shugabannin APC na reshen Kano suna cewa ko ta wani irin hali ne, sai sun san yadda suka yi suka yi nasara a takarar gwamna.

Shi gwamna bai da wannan ra’ayi, ya nuna cikakken tauhidi yayin da za a shiga takarar 2027.

Gwamnan Kano ya yaba wa Sanusi D/Tofa

A bidiyon da muka saurara a Shafin Ibrahim Adam a Facebook, an ji gwamnan yana yaba wa sabon kwamishinansa, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

A cewar gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi haƙuri da kujerar da yake kai na Darekta Janar na harkokin yada labarai a gidan gwamnati.

Duk da wasu kwamishinonin ba su fi shi ba, haka ya zauna da wannan matsayi bayan kuma gwamnan ya ce sun hana shi takarar majalisa.

Ya yi kira gare shi da ya zama mai haƙuri da jama’a kuma ya dage wajen tallata manufofi a matsayinsa na Kwamishinan Yaɗa Labarai a Kano.

Gwamna ya nemi shi ma Balarabe Sa’idu Gani ya yaƙi haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Kano kuma su yi da gaskiya da ri ƙon amana a ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng