Yan Pantamiyya Sun Gudanar da Sallar Nafila, Addu’o’i domin Neman Nasara

Yan Pantamiyya Sun Gudanar da Sallar Nafila, Addu’o’i domin Neman Nasara

  • Wasu daga cikin masoya da magoya bayan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami sun gudanar da salar nafila domin neman nasara daga Allah.
  • Magoya bayan Pantami sun roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya kare shi daga dukkan sharri, Ya kuma ba shi nasara mai albarka
  • Sun gudanar da addu’o’i domin neman taimakon Allah a harkokin siyasar Malam Pantami da sauran al’amuran rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Neman takarar Farfesa Isa Ali Pantami na ci gaba da daukar hankali bayan cire sunansa a shafin INEC.

Wasu daga cikin masoya da magoya bayanSA sun gudanar da sallolin nafila tare da addu’o’in neman taimakon Allah domin ya samu nasara.

An yi salloli da addu'o'i ga Pantami
Masoyan Isa Ali Pantami yayin addu'o'i domin samun nasararsa. Hoto: Pantami TV Concept.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Pantamiyya TV Concept ta fitar inda ta wallafa hotuna da bidiyon masoyan malamin na addu'o'i a Facebook.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulunci ta shiga batun cire sunan Pantami, ta yi kira ga Tinubu

INEC ta fitar da sunayen yan takarar gwamna

Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta cire sunayen yan takarar gwamnoni a Najeriya inda aka rasa sunan Pantami.

Lamarin ya tayarwa mabiya Malam Pantami hankali inda har wasu ke zargin ana neman yi masu zagon kasa domin hana su takara.

Bayan haka Pantami ya rubuta wa INEC wasika ta bakin lauyoyinsa inda suka ba hukumar wa'adin awanni da su mayar da sunan dan takarar.

INEC ta ba Pantami da sauransu zabi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bai wa jam’iyyun siyasa wa’adin ranar 24 ga Oktoba domin sanar da ita korafe-korafen cire sunayen ‘yan takararsu.

Ta ce wa’adin ya yi daidai da Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya bai wa jam’iyyun kwana 14 domin sanar da ita idan suna ganin an cire sunayen ‘yan takararsu bisa kuskure.

Daga cikin waɗanda ba a saka sunayensu a jerin ba akwai ‘yan takarar gwamnan Gombe da Ogun na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami da Oladipupo Adebutu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga na barazanar kashe mata da mijin da suka sace, Atiku ya yi magana

An yi wa Pantami addu'o'i a Gombe
Farfesa Isa Ali Pantami a filin jirgin saman Gombe. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Masoyan Pantami sun yi masa addu'o'i

Magoya bayan sun roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya kare Malam Pantami daga dukkan sharri, Ya kuma ba shi nasara mai albarka a harkokin siyasa da sauran al’amuran rayuwarsa.

Sun kuma roƙi Allah Ya karɓi ibadunsu da addu’o’insu, Ya tabbatar musu da alheri, tare da fatan samun nasara da albarka a dukkan al’amuransu. Amin.

Shafin ya wallafa wani faifan bidiyo da aka gano masoyan malam na addu'o'i da karatun Kur'ani domin yakar zaluncin da suke ganin an yi wa Pantami.

MURIC ta magantu kan cire Pantami a takara

Mun ba ku labarin cewa kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta bayyana cire sunan Sheikh Isa Ali Pantami daga jerin ‘yan takarar gwamna a matsayin rashin bin doka da raina kotu.

Ta buƙaci hukumar INEC ta gaggauta mayar da sunan Pantami cikin jerin, tana mai cewa cire sunan nasa ba bisa ƙa'ida ba ne kuma rashin adalci ne.

MURIC ta kuma zargi shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da nuna wariyar addini, inda ta bayyana rashin amincewarta da jagorancinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.