Gombe: Pantami Ya Fitar da Wasikar da Ya Turawa APC kafin Shiga PDP
- Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin bayani game da fita daga jam'iyyar APC da ya yi bayan zaben fitar da gwani a jihar Gombe
- Ya fadi haka ne a lokacin da ake magana kan makomar shi a jam'iyyar PDP a lokacin da ake hasashen bai fita daga APC ba
- A yanzu haka dai tsohon ministan ya karbi takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Tsohon ministan sadarwan Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya tabbatar da cewa ya fita daga jam'iyyar APC kafin shiga PDP.
Mai neman takarar gwamnan ya yi karin bayanin ne a daidai lokacin da aka rika tambayoyi kan rashin tabbas game da sauya sheka da ya yi.

Source: Facebook
Na kusa da tsohon ministan, Abba Sani Pantami ya wallafa wasikar fita daga APC da malamin ya ce ya mika wa shugaban jam'iyyar da ke mazabar shi a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Sheikh Isa Pantami ya fita daga APC
Abba Sani Pantami ya ce tun a ranar 19 ga watan Mayun 2026 Sheikh Isa Ali Pantami ya miƙa wasikar ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance.
Ya kara da cewa shugaban APC na gundumar Pantami ya sanya hannu tare da tabbatar da karɓar takardar ba tare da wata matsala ba.
A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Gombe da ma wasu wurare.
Sakon da wasikar Pantami ta kunsa
A wasikar, Sheikh Pantami ya jaddada cewa jajircewarsa na nan daram wajen ganin cigaban jihar Gombe da kyautata rayuwar al’ummarta.
Ga abin da Pantami ya rubuta a wasikar:
"Ni, Isa Ali Ibrahim Pantami, mamba a jam’iyyar APC, ina sanar da murabus dina daga kasancewa mamba a jam’iyyar.
"Na dauki wannan mataki ne sakamakon sanarwar da gwamna ya yi a bainar jama’a kan dan takarar jam’iyyar domin zabe mai zuwa, da kuma yadda reshen APC na jihar ya amince da hakan ba tare da bai wa sauran masu neman takara damar neman adalci ba.
"Yanke hukunci tun kafin lokaci ya saba wa sashe na 20 da 21 na kundin tsarin mulkin APC. Ba zan iya ci gaba da kasancewa a wata kafar da aka yi watsi da tsarin da ya dace ba.
"Na kasance mamba mai biyayya da jajircewa ga APC kuma na bayar da gudunmawa wajen bunkasarta a jihar Gombe da kasa baki daya. Saboda haka, na ajiye mukamina daga ranar da na rubuta wannan wasiƙa.
"Ina gode wa shugabannin mazaba bisa damar da suka ba ni na yin hidima, kuma ina yi wa jam’iyyar fatan alheri a ayyukanta na gaba a inda babu sabani tsakaninmu."

Source: Twitter
Yadda Pantami ya fusata kan PDP a 2011
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi bayani game da dalilin da ya sanya shi yi wa jam'iyyar PDP muguwar addu'a a 2011.
Ya bayyana cewa a lokacin da ake tsaka da rikicin Boko Haram, NSA na gwamnatin Goodluck Jonathan ya ce da hannun PDP a kashe-kashen.
Shugaban Najeriya na wancan lokacin, Goodluck Jonathan na nuna matukar mamaki kan kalaman da hadimin shi, Andew Azazi ya yi game da PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


