Kwankwaso Ya Zargi Abba da hannu a Yunkurin Hana Aminu Abdussalam Takarar Gwamna
- Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Abba Kabir Yusuf yana so INEC ta ce babu ɗan takarar gwamna a jihar Kano
- Madugu ya yi da’awar cewa da hakan bai yiwu ba, sai suka garzaya kotu domin neman a soke takarar NDC
- Kwankwaso ya sha alwashin NDC za ta yi nasara a jihar Kano sai dai idan ba a shirya zabe a shekarar 2027 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamnan Kano da kitsa shirin hana ɗan takararsu, Aminu Abdussalam Gwarzo shiga zaɓe a 2027.
Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC yana ganin da hannun Abba Kabir Yusuf a halin da takararsu ta shiga kwanan nan.

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya jefi Abba Kabir da zargi
A wata hira da ya yi da manema labarai a Kano wanda Tashar Premier Radio ta dauko, Madugu ya ce sun samu labarin abin da ake yi masu.
Da yake magana a ranar Lahadi, Rabiu Kwankwaso ya zargi Abba Kabir da fara ƙoƙarin amfani da INEC wajen cire ɗan takarar su na NDC.
Sanata Kwankwaso ya ce da hakan ya ci tura a INEC, sai gwamna ya koma amfani da kotu.
“Abin da muka tabbatar a zuciyarmu shi ne Gwamnatin jigar Kano ce ta ke makirci
"Ita ce ta tafi ta ke yin abubuwa iri-iri a INEC, suna ganin kamar yadda suke so. Daga baya INEC ta dawo da su (‘yan takaran NDC), kuma yanzu sun tafi kotu.”
- Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano ya kuma zargi wasu na kusa da gwamnan da shigar da ƙara, a dauki hayar lauyoyi domin hana su takara a 2027.
Rabiu Musa Kwankwaso ya ce:
“Duka mun san yaransu ne, mutanensu. Abin da ba su so shi ne su yi takara da wannan tafiya tamu ta Kwankwasiyya ko jam’iyyar NDC.”

Kara karanta wannan
Abba Hikima ya fito da abin da ya kamata mutane su sani kan takarar Pantami da Aminu Gwarzo
Kwankwaso bai ganin matsala a takarar Kwamred
Sai dai Kwankwaso ya dage cewa babu wani dalili na kundin tsarin mulki ko doka da zai hana ɗan takarar NDC shiga zaɓen gwamna.
’Yan takarar NDC ba su da wata matsala ta fuskar shekaru, cancantar karatu ko wasu ƙa’idojin kundin tsarin mulki in ji Kwankwaso.
‘Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ƙara zargin gwamnan da wasu na kusa da shi da ƙoƙarin guje wa karon siyasa.
2027: Kwankwasiyya tana hango nasara a Kano
A cewarsa, babu abin da zai hana su doke Gwamna Abba Kabir sai dai idan ba a shiga takara ba kamar yadda aka gani a zabukan baya.
Daily Trust ta ce Madugu ya tuna masu da tarihi, ya dauko zancen rabuwar kan da aka samu a jam'iyyar NNPP ta reshen Kano.
‘Dan siyasar ya kuma tabo batun zaman Abba gwamna da yadda ya sauya-sheka zuwa APC saboda tunanin za a taya shi magudi.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa masu zaɓe za su ƙi amincewa da abin da ya kira yunƙurin tauye musu ’yancin zaɓen wanda suke so.
Ya jaddada cewa NDC za ta shiga zaɓen kuma za ta doke abokan hamayyarta a rumfunan zaɓe duk da wahalhalun da za su ci karo da su.
Matsalar Aminu Abdussalama da INEC a Kano
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire sunan Aminu Gwarzo daga cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihar Kano.
An ji labari daga baya ta sa sunan jam’iyyar amma ba kawo sunan Gwarzo da Mustafa Kwankwaso, INEC ta yi hakan ne bisa umarnin kotu.
Idan an warware matsalar shari'a a kotun tarayya, za a iya ganin sunan 'dan takaran a shafin INEC.
Asali: Legit.ng

