Siyasar Arewa: Kotu Ta Dawo da Tsohon Gwamnan APC, Zai Yi Takarar Sanata

Siyasar Arewa: Kotu Ta Dawo da Tsohon Gwamnan APC, Zai Yi Takarar Sanata

  • Babbar Kotun Tarayya ta ayyana tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam, a matsayin halastaccen dan takarar APC na sanatan Benuea zaben 2027
  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce jam’iyyar APC ta saba doka wajen sauya sunan Suswam, duk da cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwani
  • Hukumar INEC ta tabbatar wa kotu cewa sakamakon zaben fidda gwani ya nuna Suswam ne ya samu nasara, inda ta bukaci a amince da sakamakon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, a matsayin halastaccen dan takarar jam’iyyar APC na kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas a zaben 2027.

Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, inda ya amince da hujjar Suswam cewa jam’iyyar ta sauya sunansa ba bisa ka’ida ba, duk da cewa shi ne ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada a zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

"Yadda Pater Obi da Kwankwaso za su kifar da Tinubu a zaben 2027 da taimakon Allah"

Kotu da ayyana Suswam a matsayin dan takarar APC
Tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam da ke neman takarar sanata. Hoto: Gabriel Suswam.
Source: Twitter

Mai shari’ar ya bayyana cewa matakin sauya sunan dan takarar bai yi daidai da tanade-tanaden dokar zabe da kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba, da kuma kundin tsarin mulkin APC, cewar PM News.

Yadda rikicin takarar Suswam ya fara

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1470/2026, Suswam ya bukaci kotu ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na APC domin wakiltar mazabar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas.

Tsohon gwamnan ya shigar da karar ne bayan APC ta bai wa Sanata mai ci, Emmanuel Udenbe, tikitin takarar kujerar duk da ikirarin Suswam cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwanin.

Suswam ya shigar da APC, Udenbe da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cikin karar.

Matsayar INEC kan rikicin

A zaman kotun da ya gabata, lauyan INEC, Anthony Malik, SAN, ya shaida wa kotun cewa takardun da suka shafi gudanar da zaben fidda gwani sun nuna Suswam ne ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku, an samu dan takarar da ake ganin zai kayar da Tinubu a 2027

Malik ya bukaci kotun ta yi hukunci bisa sakamakon zaben, yana mai cewa hukumar ta gabatar da rahotonta da sakamakon zaben a gaban kotu.

Ya kuma bukaci kotun ta tabbatar da sakamakon da ya nuna Suswam a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shi ma lauyan Suswam, Jibrin Okutepa, SAN, ya roki kotun ta amince da bukatun da wanda yake karewa ya gabatar.

Ya kuma bukaci kotun ta yi watsi da kalubalen farko da APC da Udenbe suka gabatar, yana mai cewa ba su da hujjar da za ta sa a amince da su.

Sai dai lauyan APC, A. G. Yirvoms, ya bukaci kotun ta amince da kalubalen jam’iyyar tare da yin watsi da karar Suswam.

A karshe, kotun ta yanke hukuncin amincewa da bukatar tsohon gwamnan, tare da tabbatar da shi a matsayin dan takarar APC na kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas a zaben 2027.

Ƙarin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.