PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fitar da Gwani a Gombe, Pantami Ya San Makomarsa

PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fitar da Gwani a Gombe, Pantami Ya San Makomarsa

  • Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya zama ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan Gombe na 2027
  • Pantami ya zama halastaccen dan takarar PDP ne bayan ya doke Garry da Mailantarki a zaɓen fitar da gwani karo na biyu da ya gudana
  • PDP ta gudanar da sabon zaben fitar da gwanin biyo bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, wanda ya rushe zaben farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya zama ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Gombe na 2027.

Pantami ya zama halastaccen dan takarar PDP ne bayan kammala tattara sakamakon zaben fitar da gwani daga ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; Ana neman hana Pantami shiga sabon fitar da gwani na PDP

Pantami.
Dan takarar gwamnan jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami lokacin da aka tabbatar masa da nasara bayan kammala tattara sakamako Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Abba Sani Pantami, daya daga cikin makusantan Pantami ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.

Pantami ya doke sauran ’yan takara biyu, Usman Aliyu Garry da Khamisu Ahmed Mailantarki, a zaɓen fitar da gwani na biyu da jam’iyyar ta gudanar ranar Talata, 29 ga watan Satumba, 2026.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a sakatariyar PDP ta jihar Gombe, Shugaban Kwamitin Zaɓen, Temnung Shekarau, ya ce Pantami ya samu ƙuri’u 2,555, yayin da Garry ya samu kuri'u 112, Mailantarki kuma ya samu 389.

Dalilin sake gudanar da zaɓen

An sake gudanar da zaɓen ne bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Gombe ta yanke ranar 24 ga Satumba

Kotun ta soke tsarin da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamna tare da umartar jam’iyyar ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bisa kundin tsarin mulkinta.

Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin bayan ƙalubalen shari’a da wasu ’yan takarar gwamna biyu na PDP, Garry da Mailantarki, suka shigar.

Kara karanta wannan

INEC na da 'yan takara ko jam'iyyar da take goyon baya a zaben 2027? An samu bayanai

Pantami ya fara zama ɗan takarar PDP ne ta hanyar amincewa da shi da murya a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar ranar 26 ga Mayu.

Ya samu tikitin ne bayan ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda a baya ya nemi tikitin takarar gwamna, bayan Jamilu Gwamna ya zama ɗan takarar da jam’iyyar ta amince da shi a matsayin ɗan takarar bai ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262