An Yi Hasashen Dukan da Tinubu Zai Sha a Arewa a Zaɓen 2027 a Wurin Atiku
- Janar John Sura mai ritaya, ɗan takarar gwamnan Plateau na ADC, ya ce Atiku Abubakar zai lashe jihohin Arewa 19 a zaɓen 2027
- Sura ya bayyana cewa ADC na samun karɓuwa a faɗin Najeriya, yana mai hasashen cewa jam’iyyar za ta lashe kujerun gwamna tsakanin 20 zuwa 25
- Ɗan takarar ya kuma zargi gwamnatin APC da gazawa wajen magance matsalar tsaro, tare da bayyana matakan da zai ɗauka idan ya zama gwamnan Plateau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Ɗan takarar gwamnan jihar Plateau a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Birgediya Janar John Sura mai ritaya, ya yi hasashen zaben 2027.
Sura ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai lashe dukkan jihohin Arewa 19 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan
"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

Source: Twitter
Sura ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar Punch, inda ya yi magana kan ƙaruwar tasirin ADC da kuma burin Atiku na zama shugaban ƙasa.
Karfin sa ADC ke da shi a Najeriya
Ya ce ADC na ƙara ƙarfi a kullum, yana mai cewa manufofin gwamnatin APC sun jawo wa jam’iyyar koma baya a idon ’yan Najeriya.
A cewarsa, yadda jam’iyyar ke samun karɓuwa a jihohi daban-daban ya nuna cewa tana da damar ƙalubalantar APC a zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa ’yan Najeriya na nuna sha’awa ga takarar Atiku da sauran ’yan takarar jam’iyyar, yana mai tabbatar da cewa suna ƙoƙarin gina tsarin da zai ba su nasara.
Sura ya ce yana da yakinin ADC za ta samu nasara a zaɓen 2027, inda ya yi hasashen cewa jam’iyyar za ta iya lashe kujerun gwamna tsakanin 20 zuwa 25.

Source: UGC
Atiku zai lashe jihohin Arewa 19

Kara karanta wannan
"Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan adawa, ya nuna ƙarfin da yake da shi a Arewacin Najeriya"
Dangane da yiwuwar haɗin gwiwar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ya rage wa Atiku ƙuri’u a Arewa, Sura ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar na da ƙarfin lashe yankin.
Sura ya ce yana da tabbacin Atiku Abubakar zai lashe dukkan jihohin Arewa 19, inda ya yi hasashen cewa mafi ƙarancin kaso da zai samu a kowace jiha shi ne kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.
Ya ƙara da cewa ADC na da damar samun sama da kaso 25 cikin 100 na ƙuri’u a yawancin jihohin sauran yankunan ƙasar.
Ya ce idan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓe cikin gaskiya tare da tabbatar da cewa ƙuri’un jama’a sun yi tasiri, Atiku zai iya samun nasara tun a zagayen farko.
An shawarci Atiku jan takara a 2027
A wani labarin, an ji cewa kungiyar CNDS ta yi gargadin cewa burin Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 na iya kawo cikas ga tsarin karba-karba.
Kungiyar ta bukaci ’yan Najeriya su ƙi amincewa da takarar Atiku, tana mai cewa ya kamata Kudu ta kammala wa’adin shekaru takwas kafin mulki ya koma Arewa.
CNDS ta ce mutunta tsarin rabon mulki na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Asali: Legit.ng