Shetttima Ya Dawo kan Peter Obi, Ya Faɗi Muƙamin da Ya Kamata Tinubu Ya ba Shi
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi mukami
- Shettima ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a Enugu ranar Asabar
- Ya kuma soki burin Obi na zama shugaban kasa, yana mai cewa ba zai iya samun isassun kuri'u daga sassan Najeriya domin lashe zabe ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi wa dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi.
Kashim Shettima ya ba Shugaba Bola Tinubu shawarar nada tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, a matsayin shugaban Hukumar Raya Kudu maso Gabas.

Source: Facebook
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam'iyyar APC a wani gangamin yakin neman zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar Enugu, cewar Arise News.

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya fasa kwai, ya tona abin da ya sa Kwankwaso yake tare da Peter Obi
Kashim Shettina ya taba Peter Obi
Mataimakin shugaban kasar ya yi suka kan burin Peter Obi na zama shugaban Najeriya, inda ya nuna shakku kan yadda zai iya samun kuri'u daga sassan kasar baki daya.
Da yake magana kan yadda Obi ke gudanar da harkokin siyasa gabanin zaben 2027, Shettima ya ce tsohon gwamnan ya kai ziyara jihohi 17 na Najeriya.
Ya bayyana cewa Obi ya ziyarci dukkan jihohin Kudu maso Gabas guda biyar, da mafi yawan jihohin Kudu maso Kudu, ban da Rivers.
Shettima ya kara da cewa dan takarar na NDC ya ziyarci Kaduna kadai a Arewacin Najeriya, sannan ya je Lagos a Kudu maso Yamma.

Source: Facebook
Gargadin da Kashim Shettima ya yiwa Obi
A cewarsa, Obi na tunanin zai yi amfani da addini wajen samun nasara a zabe kamar yadda ya yi kokarin yi shekaru hudu da suka gabata.
Shettima ya jaddada cewa ba za a iya lashe zaben shugaban kasa ta hanyar rarrabuwar kawuna ba, sai dai ta hanyar tattaunawa, sassauci da hada kan jama'a.
Ya ce babu wata kabila ko yanki da zai iya lashe zaben shugaban kasa shi kadai ba tare da kulla kawance da sauran sassan kasar ba.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa samun nasarar siyasa a Najeriya na bukatar shawarwari, fahimtar juna, yarjejeniyoyi da sadaukarwa tsakanin bangarori daban-daban.
Haka kuma, Shettima ya bayyana Kudu maso Gabas a matsayin yanki mai matukar muhimmanci ga ci gaban siyasa da tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce babu wani mutum da ya fi Shugaba Bola Tinubu zama aminin al'ummar yankin, mai goyon bayan muradunsu da kuma wanda ya yi imani da irin damar da suke da ita.
Abin da ya sa Shettima ke sukar Atiku
An ji cewa Kashim Shettima ya ce yana da damar sukar Atiku Abubakar saboda wasan da yake tsakanin Bare-bari da Fulani.
Ya ce Peter Obi, Seyi Makinde, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi duk abokansa ne duk da bambancin siyasarsu.
Shettima ya bukaci ’yan Najeriya su sake zaɓen Bola Tinubu a 2027, yana mai kare manufofin tattalin arzikinsa.
Asali: Legit.ng
