Bayan Shekaru, Amaechi Ya Fito da Yadda Suka Yi da Buhari kan Wanda Yake So Ya Gaje Shi a 2023

Bayan Shekaru, Amaechi Ya Fito da Yadda Suka Yi da Buhari kan Wanda Yake So Ya Gaje Shi a 2023

  • Rotimi Amaechi ya ce ya yi kuskuren bin shawarar marigayi Muhammadu Buhari na kada nemi goyon bayan kafin zaben fitar da gwani na APC a 2022
  • Ya bayyana cewa Buhari ya tabbatar masa a rubuce cewa zai ayyana shi a matsayin wanda yake so ya zama dan takarar jam’iyyar
  • Amaechi ya kuma zargi Tinubu da amfani da addini wajen neman goyon bayan wakilan jam’iyyar, musamman a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya dora alhakin kayen da ya sha a zaben fitar da gwani na APC na 2022 kan Shugaba Muhammadu Buhari.

Amaechi ya ce ua fadi zaben ne sakamakon shawarar da ya ce ya bi ta marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na kada ya yi wahalar neman goyon baya.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna Abba ya samu tauhidi a batun koma wa mulkin jihar Kano

Amaechi.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi da tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari Hoto,: Rt. Hon. Chibuike R. Amaechi
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Situation Room na gidan rediyon Mainland 98.3FM da ke Legas a ranar Juma’a, inda yake waiwayen yadda Shugaba Bola Tinubu ya kayar da shi.

Amaechi ya fadi abin da Buhari ya masa

Amaechi ya ce Buhari ya tabbatar masa a rubuce cewa zai bayyana shi a matsayin dan takarar da yake so ya gaje shi a zaben 2023, lamarin da ya sa ya kaurace wa neman goyon bayan wakilai da kulla kawancen siyasa kafin zaben fidda gwanin.

A cewar Amaechi, ya dauki maganar Buhari da muhimmanci saboda tsohon shugaban kasar shi ne ubangidansa, kuma ya yi imanin cewa goyon bayansa zai ba shi damar samun nasara a kan sauran masu neman takara.

Ya ce:

"Kuskure na farko da na yi a wancan zaben fitar da gwani shi ne na saurari Shugaba Buhari. Ya ce mini, ‘Kada ka sha wahalar neman goyon baya, kada ka yi komai. Zan bayyana ka a matsayin dan takarana.’

Kara karanta wannan

Babbar magana: Amaechi ya faɗi abin da zai sa ya rabu da matarsa saboda Tinubu

“Ya gaya mini hakan. Ya rubuta mini a takarda. Idan na rubuta littafina, zan fito da wannan takarda.”

Rashin kulla kawance ya shafi Amaechi

Tsohon ministan sufuri ya ce shawarar da ya yanke na kin kulla yarjejeniyar rabon mukamai da gwamnoni da sauran manyan jiga-jigan APC ta yi tasiri wajen durkusar da burinsa, inda ta bai wa Tinubu damar kulla kawance kafin zaben fidda gwani.

Amaechi ya bayyana cewa da ya yi alkawarin ba wasu gwamnoni mukamai, ciki har da na mataimakin shugaban kasa da sakataren gwamnatin tarayya, da watakila ya samu goyon bayansu.

Ya ce:

“Ban kulla yarjejeniyoyi ba. Da na yi hakan, da na iya yi maka alkawarin mukamin mataimakin shugaban kasa ko sakataren gwamnatin tarayya, sannan na shiga zaben fitar da gwani, watakila da na yi nasara. Da na samu gwamnoni a bayana.
“Saboda ban kulla yarjejeniya ba, Tinubu ya samu damar yin hakan.”

Amaechi ya zargi Tinubu

Amaechi, wanda shi ma ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a zaben fitar da gwani na APC na 2022, ya kuma zargi Tinubu da amfani da raddini wajen samun goyon bayan wakilan jam’iyyar, musamman a Arewa.

Kara karanta wannan

Yadda Obasanjo ya yi kutun kutun domin hana Amaechi zama gwamnan Rivers

Sai dai ya ce ba zai yi amfani da addini a matsayin hanyar neman kuri’u ba, yana mai cewa matsayarsa na nuna kishin kasa da hadin kan ‘yan Najeriya.

Ya kuma ambaci tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya ce a baya ya goyi bayan burinsa na zama shugaban kasa, kafin daga bisani ya koma bayan Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262