Wike Ya Tada wa Gwamnonin APC 3 Hankali da Yan Takaran da Ya Kawo Jihohinsu

Wike Ya Tada wa Gwamnonin APC 3 Hankali da Yan Takaran da Ya Kawo Jihohinsu

  • Gamayyar Rainbow Coalition ta Nyesom Wike na haifar da rikici a APC a jihohin Imo, Kwara da kuma Gombe gabanin zaɓen 2027
  • Ministan ya dage ƙungiyar za ta taimaka wa Bola Tinubu ya sake lashe zaɓe, amma za ta iya goyon bayan ’yan takarar PDP a wasu zaɓukan
  • Duka gwamnonin da suke yaƙar gamayyar Rainbow Coalition sun fito neman takaran kujerun Majalisar dattawa a ƙarƙashin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tafiyar Rainbow Coalition da ake dangantawa da Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ta razana gwamnonin APC.

Gamayyar ta tashi hankali a cikin jam’iyyar APC, musamman a jihohin Imo, Kwara da Gombe, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Gwamnonin APC
Gwamnonin APC wajen kamfen Bola Tinubu a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Rahotanni daga Leadership sun nuna cewa wasu ’yan jam’iyyar APC da aka fusata saboda takara suna iya tsallaka su taimaki jam’iyyun hamayya.

Ko da sun bar APC, za su ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zarce a mulki.

Kara karanta wannan

An samu rudani a APC da mutane 2 suka ‘lashe’ zaben zama ‘dan takaran sanata

Gwamnan Imo na ƙoƙarin kare muradun APC

A jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, ya nuna adawarsa da duk wani shiri da zai iya raunana ’yan takarar su.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama kan kujerar Sanatan Imo ta Yamma, bayan tsohon gwamna Rochas Okorocha ya samu nasara a kotu.

Uzodimma ya nuna cewa zai ƙalubalanci wannan hukunci domin ganin bayan Okorocha, wanda ake ganin cewa layinsu guda da Ministan harkokin birnin Abuja.

Gwamnan ya musanta kasancewar ƙungiyar Rainbow Coalition a Imo, wanda ya nuna sun sha bam-bam da abokin rigimar takarar shi a yankin Imo ta yamma.

An ce ya yi barazanar ƙwace motocin da aka bai wa wasu mambobin ƙungiyar tallata Tinubu idan suka yi aiki da zai cutar da ’yan takarar jam’iyya mai-ci.

Mustapha da Saraki suna yaƙar APC a Kwara

A jihar Kwara, siyasar jihar ta ɗauki sabon salo bayan Sanata Saliu Mustapha ya zama ɗan takarar PDP, bayan ficewarsa daga APC sakamakon rikicin takara.

Kara karanta wannan

APC ta yi wa Gwamna ƙarfa ƙarfa, ta cire shi a cikin kwamitin kamfen Tinubu

Mustapha ya ƙaddamar da ƙungiyar Otoge Progressives Rainbow Coalition, ya tabbatar da tarayyarsa da tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki.

Wike ya soki Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan yadda APC ke zaɓen ’yan takara, yana zarginsa da yin watsi da sanatoci da ’yan Majalisar tarayya.

Saboda haka ya ce ya kamata ’yan siyasar da ba su gamsu da APC ba su samu damar tsayawa takara a wasu jam’iyyu, yayin da suke goyon bayan Tinubu.

A Kwara ma mutanen Wike sun tada hankalin AbdulRazaq wanda wa’adinsa ya zo karshe kuma ya ci burin zama sanata mai wakiltar mazabar tsakiyar jihar a 2027.

Fitowar Pantami ta ƙara dagula siyasar Gombe

A jihar Gombe, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya zama ɗan takarar PDP bayan barin APC a watan Mayu.

Wike ya bayyana cewa bai san Pantami ba, duk da rahotanni suna nuna kusancinsa da tsagin ministan.

Dawowar Pantami cikin ‘yan takarar gwamna ta birkita lissafin su Gwamna Inuwa Yahaya wanda bai zaman lafiya da su Sanata Danjuma Goje a cikin APC.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jibga mutane 3000 a kwamitin yakin zabe don nasarar Tinubu da APC

TND ta soki tsarin shinkafa da waken Wike

Wata ƙungiyar farar hula ta The News Direction (TND) ta soki Nyesom Wike, tana mai cewa abin da yake yi na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya.

Babban daraktan ƙungiyar, Chris John Alofu, ya bayyana cewa ƙungiyar Rainbow Coalition wani shiri ne da Wike ke ginawa domin cimma burinsa a 2031.

Ya yi gargaɗin cewa wannan na iya rage wa Tinubu damar samun nasara a zaɓe, saboda tsoron jawo saɓani tsakanin shugaban ƙasa da gwamnonin APC.

Kamfen Bola Tinubu a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Nyesom Wike da Bola Tinubu a lokacin kamfen APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Minista yana ganin za a rage masu aiki

Festus Keyamo yana ganin babu abin da zai faru don an hana Atiku Abubakar, shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

An rahoto Ministan harkokin jiragen yana sukar Atiku Abubakar saboda ya ki gamsuwa da hukuncin kotun da ya rusa takarar shi a ADC.

Festus Keyamo yana da ra'ayin cewa ƙarfi aka yi amfani da shi wajen raba Nafiu Bala da jam'iyya, aka damƙa ta a hannun David Mark.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng