Yan Bindiga Sun Shammaci Dan Sanda Yana tsaka da Salla a Titi, Sun Hallaka Shi
- Mahara sun yi wa Taura a Jihar Jigawa hari, inda suka kashe wani ɗan sanda da ke sallar dare a bakin shingen binciken ababen hawa
- Lamarin ya sake bayyana haɗarin da jami’an tsaro ke fuskanta, tare da ƙara nuna alamun tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar
- Ya kamata hukumomi su ɗauki matakin gaggawa domin hana ’yan bindiga samun gindin zama a Jigawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Taura, Jigawa - Wasu yan bindiga sun kai hari a jihar Jigawa inda wani daga cikin yan sanda ya rasa ransa yayin farmakin.
An kai harin ne a daren jiya, lokacin da wasu ’yan bindiga suka farmaki wani shingen binciken ababen hawa a Taura.

Source: Original
Yadda aka kashe dan sanda yana salla
Majiyoyi daga Bakatsine a X, wani mai sharhi kan lamuran tsaro ya ce miyagun sun kashe ɗan sandan da ke tsaye wajen gudanar da salla.
Wannan hari ya zama wani abin tunatarwa kan irin haɗarin da jami’an tsaro ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu, musamman a wuraren da ake fama da matsalolin tsaro.
Lamarin ya kuma nuna alamun yadda matsalar ’yan bindiga ke neman yaɗuwa zuwa wasu yankunan Jigawa, wadda a baya ake kallonta a matsayin jihar da ta fi samun kwanciyar hankali.
Ya kamata harin ya zama babban gargaɗi ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar, domin kada su jira matsalar ta ƙara kamari kafin ɗaukar matakan da suka dace.
Wajibi ne hukumomi su ƙarfafa tsaro, kare al’ummomin yankin tare da hana ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai samun mafaka ko kafa sansanoni a jihar.
Majiyar ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, tare da ba iyalansa da abokan aikinsa haƙurin jure wannan rashi.
Haka kuma, al'umma sun yi addu'o'i inda suka roƙi Allah Ya tona asirin waɗanda suka aikata wannan ta’asa, Ya kare al’ummar Taura da yankunan da ke makwabtaka da ita, Ya kuma hana Jigawa zama wata fagen fama da ’yan bindiga.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng

