"Haka Allah Ya Tsara," 'Dan Takarar APC, Jamilu Gwamna Ya Nemi Hadin Kan Pantami a Gombe
- 'Dan takarar gwamna da APC ta tsaida a jihar Gombe, Jamilu Gwamna ya bukaci mambobin jam'iyyarsa su jingine duk wani sabani
- Gwamna ya bayyana cewa Allah SWT ke ba da mulki ga wanda ya so, yana mai kira ga sauran wadanda suka nemi takara su zo a hada kai
- Wannan kira na zuwa ne yayin fa tsohon ministan sadarwa, Isa Pantami ya lashi takobin yakar abin da ya kira 'zalunci' a tsarin tsaida dan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria – Dan takarar gwamna na APC a jihar Gombe, Dr Jamil Isiyaka Gwamna, ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su manta da sabanin da ke tsakaninsu, su hada kai don tunkarar zaben 2027.
Ya yi wannan kira ne yayin da aka fara samun sabani da nuna fushi daga wasu ‘yan jam’iyyar musamnan masu neman takarar gwamna kan tsarin sulhu da ya ba shi tikitin takara.

Source: Facebook
Jamlu Gwamna ya nemi hadin kai a APC
A rahoton Daily Trust, Jamilu Gwamna ya bukaci tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami da sauran wadanda suka nuna sha'awar takara su jingine duk wani sabani don ciyar da APC gaba.
Gwamna ya ce:
"Ina kira ga dukkan ‘yan jam’iyyarmu ta APC, wadanda suka nemi takara da wadanda suka goyi bayan wasu, da su zo mi hada kai domin ci gaban jam’iyya.”
Ya jaddada cewa hadin kai na da matukar muhimmanci domin samun nasara a dukkan kujerun da za a fafata a zabe.
Abin da ya ba Gwamna nasara a Gombe
Ya ce jam’iyyar APC na da damar lashe zaben shugaban kasa, gwamna, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da na jihohi idan aka tabbatar da hadin kai a cikin gida.
Dan takarar ya danganta nasararsa da ikon Allah, yana mai kira ga wadanda ba su ji dadi ba da su amince da sakamakon a matsayin kaddara.
“Mulki na Allah ne, yana ba wanda ya ga dama a lokacin da ya ga dama," in ji shi.
Ya kara da cewa mutum daya ne kawai zai iya rike mukami a lokaci guda, don haka wadanda suka sha kaye su jira wani lokaci na gaba.
Martani daga wasu ‘yan takara
Duk da haka, wasu daga cikin masu neman takarar sun nuna rashin amincewa da tsarin sulhu, ciki har da tsohon minista, Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda ya bayyana tsarin a matsayin “na nadin sarauta.”
Ya ce tsarin ya sabawa ka’ida, yana mai cewa za su bi hanyoyin doka da na jam’iyya domin kalubalantar lamarin, kamar yada Leadership ta ruwaito.

Source: Facebook
A karshe, Jamilu Gwamna ya kuma gode wa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarar tsarin tsaida dan takara.
Ya bukaci dukkan ‘ya'yan jam’iyya da su ci gaba da goyon bayan APC domin tabbatar da ci gaban jihar Gombe.
Gombe: APC ta kare matakin da ta dauka
A baya, kun ji cewa APC ta yi bayani kan matakin da ta dauka na fitar da 'yan takara ta hanyar masalaha a jihar Gombe yayin da ake tunkarar zaben 2027.
APC ta ce tsarin sulhu yana daga cikin abubuwan da kundin tsarin jam'iyya ya amince da su, kuma yana taimakawa wajen rage rikice-rikice da kashe kudi a lokacin zaben fidda gwani.
Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa duk wanda bai gamsu da tsarin sulhu ba, zai iya shiga zaben fitar da gwani kai tsaye kamar yadda doka ta tanada.
Asali: Legit.ng


