Dan Majalisa a Borno Ya Fashe da Kuka, Ya Roki a Bari Ya Sake Komawa Kujerarsa

Dan Majalisa a Borno Ya Fashe da Kuka, Ya Roki a Bari Ya Sake Komawa Kujerarsa

  • Ana ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027, yayin da masu neman takara ke kara kamun kafa domin cika burin da suke da na samun mulki
  • Wani dan majalisar dokokin jihar Borno, Hon Audu Mustapha Ganga, bai yi kasa a gwiwa ba wajen neman ya sake zarcewa kan kujerarsa
  • Dan majalisar na jam'iyyar APC wanda ya kwashe shekaru a kan kujerar, ya roki masu ruwa da tsaki na mazabarsa da su sake ba shi dama

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Magumeri a majalisar dokokin jihar Borno, Hon. Audu Mustapha Ganga, ya mika koka bararsa ga mutanen mazabarsa.

Dan majalisar dokokin ta jihar Borno ya roƙi mutanen mazaɓarsa da su amince da takararsa ta wa’adi na biyar, domin ci gaba da wakiltarsu.

Kara karanta wannan

Pantami zai yi yaki da zalunci wajen fitar da dan takarar gwamnan APC a Gombe

Dan majalisa ya yi kuka a Borno
Audu Mustapha Ganga tare da fom din neman takara na APC Hoto: Grema Ali Wakilbe
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa dan majalisar ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta.

Audu Mustapha Ganga ya yi kuka

A cikin bidiyon wanda shafin Lapai Tv ya sanya a Facebook, dan majalisar ya fashe da kuka yayin da yake jawabi a gaban mutanen da ke wajen.

Dan majalisar, wanda ya kwashe shekaru 16 a kan wannan kujera, ya fashe da kuka yayin da yake roƙon masu ruwa da tsaki daga mazaɓarsa waɗanda ke kiran da a samar da sabon wakilci.

“Kun san ni ɗan talakawa ne, amma na samu damar yi muku abubuwa da dama. Ina muku alƙawarin ba ku wakilci mafi kyau idan aka sake ba ni dama."

- Hon. Audu Mustapha Ganga

Dan majalisar na fuskantar kalubale

Tuni dai Hon. Audu Mustapha Ganga ya sayi fom na jam'iyyar APC, domin sake tsayawa takara a kokarin da yake yi na ci gaba da wakiltar mutanen mazabarsa.

Kara karanta wannan

"Mulki na Allah ne": Mataimakin shugaban majalisa ya hakura da neman kujerar sanata Ndume

Majiyoyi sun bayyana cewa tuni wasu masu neman takara shida suka sayi fom ɗin na gani ina so da na tsayawa takara domin ƙalubalantar takararsa.

Dan majalisa ya yi kuka a Borno
Dan majalisa mai wakiltar Magumeri a majalisar dokokin Borno, Audu Mustapha Ganga Hoto: Real Usman Korimi
Source: Facebook

An yi martani kan kukan dan majalisar

Sai dai, kukan da ya yi ya haifar da martani daban-daban a kafofin sada zumunta.

Abubakar Hassan ya ce:

“Yanzu ne ka san cewa kai ɗan talakawa ne bayan ka nuna rashin mutunci ga shugabanninka, ka sani cewa gwamna ba zai raga maka ba.”

Mu’azu Hassan ya ce:

"Babu sauƙi samar da abinci ga iyali. Babu abinci ga rago.”

Lawan Modu ya ce:

"Hon. Ganga ya taɓa rayuwar matasa da mata ta hanyar samar da ayyukan yi da tallafi. Zubar da hawaye ba alamar rauni ba ne.”

Muhammad Abba Kura ya ce:

"Kukan makirci kake yi.”

Tinubu ya umarci Ayade ya hakura da takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya janye daga yunkurin neman takarar kujerar sanata.

Ben Ayade wanda ya yi mulki daga shekarar 2015.zuwa 2023, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya umarci ya janye daga takara.

Ben Ayade dai ya nuna sha'awar neman tikitin jam'iyyar APC na takarar kujerar sanata mai wakiltar Cross River ta Arewa a babban zaben 2027, amma daga bisani ya janye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng