Shin da Gaske Pantami Ya Wulakanta Sarkin Gombe? An Tsage Gaskiya

Shin da Gaske Pantami Ya Wulakanta Sarkin Gombe? An Tsage Gaskiya

  • Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu-Abubakar III, ta yi magana kan batun hana Sarkin ganawa da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami lokacin da yake Minista
  • Fadar ta ce zargin ba shi da tushe, an yi shi ne saboda dalilan siyasa tare da kokarin haifar da rashin jituwa
  • Ta kuma gargadi masu yada bayanan da ke cin mutuncin Sarkin, tana mai cewa za ta iya daukar matakin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu-Abubakar III, ta karyata zargin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa an hana Sarkin ganawa da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, lokacin da yake kan mukamin Minista.

Fadar ta bayyana zargin a matsayin mara tushe, wanda aka yi saboda dalilan siyasa tare da nufin haifar da tashin hankali ba tare da wani dalili ba.

Kara karanta wannan

'Atiku da Amaechi, Peter Obi da Kwankwaso ba za su iya samun nasara a zaben 2027 ba'

Fadar Gombe ta musanta zargin da aka yi kan Pantami
Mai martaba sarkin Gombe da Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Masoyin Sarkin Gombe, Prof Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Fadar Sarkin Gombe ta bayyana hakan ne ta hannun Ajiya Masu Gombe kuma shugaban Dandalin Matasan Lamurde Gombe, cewar rahoton jaridar PR Nigeria.

Ta kuma jaddada cewa Sarkin Gombe da Farfesa Pantami sun dade suna da kyakkyawar alaka mai cike da mutunta juna.

Fadar Gombe ta musanta zargin

Rahotanni sun nuna cewa Affan Buba Abuya, tsohon hadimin Farfesa Pantami, ne ya yi zargin a wani rubutu da ya wallafa a kafafen sada zumunta.

A cewar zargin, an hana Sarkin Gombe damar ganawa da tsohon ministan a lokacin da yake cikin Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Ajiya Masu Gombe ya ce bayanan ba gaskiya ba ne kuma za su iya rage martabar da ake bai wa sarakunan gargajiya.

“Ina so na bayyana karara cewa bai kamata kowa ya rika yin zarge-zarge marasa tushe ko marasa amfani a kan Sarkin ba. Abin da aka fada game da Sarkin Gombe karya ce tsagwaronta. Sarkin mutum ne mai girma kuma jagora mai mutunci. Bai taba faruwa an hana shi ganawa da Farfesa Pantami ba.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Kano za ta karbi manyan baki, akwai babban taro a kan miyagun kwayoyi

Alakar Sarkin da Pantami

Ajiya ya jaddada cewa Sarkin Gombe da tsohon ministan sun kasance cikin alakar mutunta juna.

Ya ce kokarin nuna cewa akwai sabani a tsakaninsu yana da nufin haifar da rarrabuwar kai saboda dalilan siyasa.

Fadar ta kuma gargadi mutane kan yada bayanan da take ganin suna nuna rashin girmamawa ga Sarkin Gombe. Ta ce irin wannan dabi’a ta saba wa al’adu da kyawawan dabi’un al’ummar Gombe.

Fada ta yi barazanar shari’a

Ajiya ya ce fadar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a a kan duk wanda aka samu da gangan yana bata sunan Sarkin Gombe.

Ya ce matsayin mutum a al’umma ko siyasarsa ba za su hana fadar neman hakkinta ba.

“Za mu iya daukar matakin shari’a a kan kowa, ko wanene shi, domin wannan batu ya shafi mutunci da kimar Sarkinmu.” In ji shi.

Ya kuma soki kokarin jawo sarakunan gargajiya cikin siyasar bangaranci. A cewarsa, ya kamata ‘yan siyasa da magoya bayansu su gudanar da yakin neman zabensu cikin ladabi da girmamawa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji asalin dalilin dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi 3 a Kano

Sarkin Gombe ya yi magana kan Pantami
Mai martaba sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III Hoto: Masoyin Sarkin Gombe
Source: Facebook

Pantami ya samu goyon baya a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren jam'iyyar ADC na ƙaramar hukumar Gombe, Hon. Babangida Usman, wanda aka fi sani da Babangida Ventures, ya yi murabus.

Ventures ya sauya sheƙa zuwa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami baya a takararsa ta gwamnan Gombe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng