Gwamna Ya Fitar da N3.5bn, Zai ba Alhazan Jiharsa Rancen Kudin zuwa Aikin Hajji
- Gwamnatin Jigawa ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 3.5 ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai domin biyan kuɗin ajiyar Hajjin 2027 ga maniyyata
- Kuɗin rancen zai taimaka wa maniyyata 466 daga jihar tare da bai wa Jigawa damar cika wa'adin da Hukumar Alhazai ta Kasa ta gindaya
- Gwamnati ta ce biyan kuɗin da wuri zai sauƙaƙa shirye-shiryen masauki, sufuri, abinci da sauran hidimomin aikin Hajjin shekarar 2027 cikin nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jigawa – Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 3.5 ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar domin biyan kuɗin ajiyar aikin Hajjin shekarar 2027 ga maniyyata daga jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al'adu na jihar, Sagir Musa, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan matsayar majalisar bayan zamanta da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse.

Source: Twitter
Maniyyata 466 za su ci gajiyar rancen
A cewarsa, matakin ya nuna ƙudirin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta tare da kula da walwalar al'ummar Jigawa, in ji rahoton Punch.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa jihar ba ta rasa damar da aka ware mata a aikin Hajjin shekarar 2027.
Sagir Musa ya ce rancen zai bai wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai damar biyan kuɗin ajiyar Hajji ga maniyyata 466 daga jihar cikin wa'adin da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta tsara.
Ya ce:
"Majalisar ta amince da bayar da rancen Naira biliyan 3.5 ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai domin sauƙaƙa biyan kuɗin ajiyar Hajjin 2027 ga maniyyata 466 daga jihar."
Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin zai taimaka wa jihar wajen bin umarnin NAHCON, wanda ya bukaci jihohi su kammala biyan kuɗaɗen ajiyar Hajji da wuri domin Saudiyya ta fara shirye-shiryen kwangilolin aikin Hajjin bana.
Dalilin biyan kuɗin Hajjin da wuri
A cewar gwamnatin jihar, biyan kuɗin ajiyar Hajji da wuri zai taimaka wajen tabbatar da kujerun jihar da kuma sauƙaƙa shirye-shiryen masauki, sufuri, abinci da sauran muhimman hidimomin da maniyyata za su buƙata yayin aikin Hajji.
Sagir Musa ya ce majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a matsayin wata dabarar tabbatar da ingantaccen tsari da gudanar da dukkan shirye-shiryen aikin Hajjin 2027 ba tare da tangarɗa ba.
Ya buƙaci dukkan maniyyatan da abin ya shafa su haɗa kai da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar ta hanyar cika dukkan sharuddan rajista da bin wa'adin da aka tsara domin kauce wa jinkiri.
Majalisa ta amince da wani aiki
Baya ga amincewa da wannan rance, kwamishinan ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta kuma amince da ware kuɗaɗe domin gyaran wata makarantar gyaran hali da ke jihar.
Sai dai bai bayyana adadin kuɗin da aka ware domin aikin ba ko kuma lokacin da za a fara aiwatar da shi.
Gwamnatin jihar ta ce tana ci gaba da ɗaukar matakan da za su inganta ayyukan gwamnati da kuma tabbatar da cewa al'ummar Jigawa suna cin gajiyar shirye-shiryen da ake aiwatarwa a fannoni daban-daban.
Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tarayya domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin tsari da nasara, tare da tabbatar da jin daɗin maniyyatan jihar tun daga lokacin rajista har zuwa dawowarsu gida bayan kammala ibadar Hajji.
Asali: Legit.ng


