Wike Ya Sace Gwiwoyin Atiku kan Daukar Amaechi a Matsayin Abokin Takara a 2027
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce zaben Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar ba zai kara wa ADC karfi a zabe ba
- Wike ya ce Amaechi na iya zama mai amfani ta fuskar samar da kudi, amma ba shi da tasirin da zai kawo kuri’u
- Tsohon gwamnan na Rivers ya ce Amaechi bai nuna yana da karfin lashe zabe a jihar tun bayan 2011 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi magana kan zabin da Atiku Abubakar ya yi na Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.
Wike ya ce zabin Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na ADC, ba zai kara wa jam’iyyar damar samun nasara a zabe ba.

Source: Facebook
Wike ya bayyana haka ne yayin ganawar da yake yi da kafafen yada labarai duk wata a Abuja ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton TheCable.
Ya ce ko da yake zaben Amaechi na iya zama mai amfani ta fuskar samar da kudi domin yakin neman zabe, tsohon ministan ba shi da tasirin siyasa da zai iya kawo kuri’u.
Wike ya yi magana kan Atiku
“Bari na fara da batun Amaechi da aka zaba a matsayin mataimakin Atiku. Wani lokaci, bari na fada muku cewa, hakika zai yi wa Atiku wahala ya zama shugaban kasa.”
“Duk lissafin da yake yi... idan za ka zabi mataimakin shugaban kasa, na tabbata abin da zai iya sa ka zabi Amaechi shi ne bangaren kudi. Amma idan maganar ita ce kawo kuri’u domin mara wa Atiku baya, to batun ya mutu tun kafin ya fara.”
Wike ya soki tasirin Amaechi
Ministan ya ce Amaechi bai nuna yana da tasirin da zai iya kawo kuri’u a jihar Rivers tun bayan 2011 ba.
“Na doke shi sosai. Bai taba lashe zabe ba tun bayan 2011, lokacin da nake daraktan yakin neman zabensa.”
“Shi ne daraktan yakin neman zaben Buhari a 2015, lokacin yana gwamna. Amma Buhari bai samu 25% ba.”
“Ya sake zama daraktan yakin neman zabe a 2019, lokacin yana minista. Buhari bai samu 25% ba. Ya goyi bayan Atiku a 2023, amma Atiku bai samu 15% ba.”
- Nyesom Wike
Wike ya kalubalanci matsayin Amaechi
Wike ya ce kasancewar mutum tsohon gwamna kawai ba ya nufin zai zama babban jari ga jam’iyya a siyasance, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Yanzu bari na tambaye ku, a ina ne yake da amfani? Ga jihar Rivers da yankin Kudu maso Kudu? Kasancewarka tsohon gwamna kawai ba ya sa ka zama babban jari. Ba maganar cewa ni tsohon kaza ne ko tsohon wane ba ce.”
- Nyesom Wike
Ministan ya ce ya kamata a auna tasirin dan siyasa ne bisa karfinsa na rike magoya baya da kuma irin nasarorin da ya samu a aikace.

Source: Twitter
Wike ya zargi Amaechi da yin baki 2
Wike ya kuma zargi Amaechi da sauya matsayinsa, inda ya ce tsohon ministan ya amince ya shiga tsarin zaben da ya taba sukar yadda ake gudanar da shi.
Ya kara da cewa:
“Wannan shi ne mutumin da wata guda da ya wuce ya ce an samu kura-kurai a zaben fitar da gwani na ADC.”
“Shi ne kuma mutumin da yake cin gajiyar abin da ya kira rashin gaskiya da kura-kuran da ke cikin wannan tsari, amma ba mu ce komai ba.”
Wike ya kalubalanci Onaiyekan
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kalubalanci tsohon Archbishop na Cocin Katolika na Abuja, Cardinal John Onaiyekan.
Wike ya ce malamin addinin bai kasance wanda bai goyi bayan wani bangare ba a lokacin babban zaben Najeriya na shekarar 2023.
Asali: Legit.ng


