2027: APC Ta Kwantar da Hankalin Pantami, Ta ba Shi dama kan batun Takarar Gwamna a Gombe

2027: APC Ta Kwantar da Hankalin Pantami, Ta ba Shi dama kan batun Takarar Gwamna a Gombe

  • APC ta yi bayani kan matakin da ta dauka na fitar da 'yan takara ta hanyar masalaha a jihar Gombe yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • Mai magana da yawun APC na jihar Gombe, Moses Kyari ya ce duk dan takarar da bai gamsu da tsarin sulhu ba, zai iya fitowa a yi zaben fidda gwani
  • Wannan na zuwa ne bayan Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami da Sanata Danjuma Goje sun nuna ba su yarda ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe – Jam’iyyar APC a jihar Gombe ta kare matakin da ta dauka na amfani da tsarin sulhu wajen zaben ‘yan takarar da za su gwanza a zaben 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne bayan ta sanar da sunayen ‘yan takarar da aka amince da su ta hanyar sulhu domin zaben gwamna, majalisar dokoki ta kasa da ta jiha.

Kara karanta wannan

Bayan Pantami, Goje da Sanata Alkali sun yi watsi da 'yan takarar APC a Gombe

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa da harkokin tattalin arzikin zakani, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Pantami
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa sai dai matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu daga cikin masu neman takara da sun nuna rashin amincewarsu a fili.

Sanata Danjuma Goje, Sanata Anthony Siyako Yaro, tsohon ministan sadarawa, Farfesa Isa Ali Pantami da Sa’idu Ahmed Alkali sun slyi fatali da tsarin, inda suka ce an karaya doka.

Dalilin amfani da tsarin sulhu

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na APC a jihar, Moses Kyari, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an dauki matakin ne domin karfafa hadin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.

Ya ce tsarin sulhu yana daga cikin abubuwan da kundin tsarin APC ya amince da su, kuma yana taimakawa wajen rage rikice-rikice da kashe kudi a lokacin zaben fidda gwani.

Sanarwar ta ce:

“Jam’iyya na son ta bayyana gaskiya domin gyara duk wata fahimta mara kyau da ake yadawa. Kundin tsarin APC ya amince da tsarin sulhu a matsayin hanya mafi dacewa domin tsaida ‘yan takara, domin yana karfafa hadin kai da rage sabani.”

Kara karanta wannan

Pantami ya yi martani da APC ta yi amfani da tsarin 'sulhu' a tsayar da ɗan takara

Yadda APC ta kare kanta a Gombe

Kyari ya ce an gudanar da tattaunawa mai fadi da bangarori daban-daban da suka hada da dattawan jam’iyya, kwamitin gudanarwa na jiha da kuma dukkan masu neman takara.

Ya kara da cewa an gayyaci duk masu neman takara su halarci tsarin, amma wasu daga cikinsu sun zabi kauracewa.

“Abin mamaki ne yadda wadanda suka ki shiga tsarin yanzu suke kalubalantar sakamakon da ba su taimaka wajen samar da shi ba," in ji shi.
Jam'iyya.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da aka kafe a ofishsinta a Abuja Hoto: OfficialPDPNig
Source: Twitter

Damar da APC ta ba Pantami, Goje

Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa duk wanda bai gamsu da tsarin sulhu ba, zai iya shiga zaben fidda gwani kai tsaye kamar yadda doka ta tanada, in ji rahoton Vanguard.

“Duk dan takarar da bai amince da tsarin ba zai iya fitowa neman takara, sai a fafata a zaben fidda gwani kai tsaye, inda kowa zai samu dama iri daya,” in ji shi.

APC ta kuma bukaci ‘yan takara da magoya bayansu da su guji furuci ko matakin da zai iya kawo rabuwar kai ko illa ga nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Pantami ya san makomarsa: APC ta tsayar da ɗan takarar gwamnan Gombe

Pantami ya yi fatali da sulhun Gombe

A baya, kun ji cewa taohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya yi watsi da tsarin sulhun APC da aka sanar a Gombe.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa tsohon minista, Pantami yana Abuja lokacin da labarin sulhun ya bayyana, lamarin da ya ayyana a matsayin wanda ya sBa wa doka.

Pantami ya ce doka ta tanadi cewa dole ne duk masu neman takara su amince kafin a yi sulhu, in ba haka ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262