Bayan Sako Malamai a Gaba, Ibrahim Dahiru Bauchi Ya Je wajen Tinubu a Abuja

Bayan Sako Malamai a Gaba, Ibrahim Dahiru Bauchi Ya Je wajen Tinubu a Abuja

  • Khalifa Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya kai ziyarar girmamawa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da miƙa masa goron gayyatar Mauludi
  • An shirya gudanar da babban taron Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani a ranar 9 ga Agustan 2026 a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano
  • Khalifan Dahiru Bauchi ya ce za a yi addu'o'in neman zaman lafiya, haɗin kai da kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Khalifa Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya kai ziyarar girmamawa ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya miƙa masa goron gayyata domin halartar babban Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani.

Khalifan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa, inda ya ce ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban ƙasar yayin ziyarar.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya nuna ɓacin ransa kan cin zarafin Musulmai yan ƙabilar Igbo

Ibrahim Dahiru Bauchi Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Ibrahim Dahiru Bauchi yayin ganwa da da Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Khalifah Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Ibrahim Dahiru Bauchi ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa an shirya gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 9 ga Agustan 2026, da ƙarfe 10:00 na safe a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Yadda za a gudanar da Mauludi

Khalifa Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya ce taron zai haɗa malamai, shugabannin addinai, jami'an gwamnati, sarakunan gargajiya da dubban mabiya daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.

Ya ce manufar taron ita ce tunawa da Allah, girmama rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAW), tare da tuna gudunmuwar Sheikh Ahmad Tijjani ga addinin Musulunci.

Khalifan ya kuma yaba wa shugaban ƙasa da gwamnatinsa bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin inganta zaman lafiya, haɗin kan addinai da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Kiran halartar taron da addu'a

Khalifan ya yi kira ga mabiya ɗariƙar Tijjaniyya, masoya Annabi Muhammad (SAW) da sauran masu fatan alheri da su halarci taron.

Kara karanta wannan

Izala ta shirya babban taro a Abuja, Bala Lau ya gayyaci Sheikh Jingir

Ya bayyana cewa ana sa ran taron zai ƙarfafa imani, soyayya da haɗin kai tsakanin al'umma tare da bunƙasa zaman lafiya.

Haka kuma ya ce mahalarta za su yi addu'o'i na musamman domin Allah Ya kawo ƙarshen rikice-rikice, rashin tsaro, rarrabuwar kawuna da sauran ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Khalifa Ibrahim Dahiru Bauchi
Khalifa Ibrahim Dahiru Bauchi yana huduba. Hoto: Khalifah Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauch
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa za a kuma roƙi Allah Ya kare ƙasar, Ya shiryar da shugabanni, Ya tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa ga Najeriya baki ɗaya.

Ziyara zuga a Bola Tinubu na zuwa ne bayan bishop bishop sun ziyarce shi sun tsage masa gaskiya, lamarin da ya sa wasu suke ganin kamar malaman Musulunci ba su yi haka ba.

Sai dai Sheikh Mansur Sokoto ya bayyana cewa su ma sun kai wa shugaban kasa irin ziyarar kuma sun fada masa gaskiya.

Wike ya gargadi bishop bishop

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gargadi shugabannin Cocin Katolika kan zargin cewa Hukumar INEC ba ta da adalci.

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

Nyesom Wike ya bayyana cewa irin waɗannan kalamai ba tare da hujjoji ba na iya rage amincewar jama'a da tsarin zaɓe na Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa shugabannin addinai su kasance masu taka-tsantsan wajen yin kalamai kan muhimman batutuwan ƙasa saboda tasirin da suke da shi a cikin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng